IQNA

Musulmi A Birnin New Delhi Na Kasar India Sun Gudanar Da Tarukan Idul Mab’as

Bangaren al’adu da fasaha, mabiya addinin musulunci na kasar India sun gudanar da taron idul mab’as wato ranar aiko manzon Allah tsira da amincin Allah su tabbata a gare shi daiyalan gidansa tsarkaka da kuma muhimman darussan da ke cikin wannan sako mai tsari da manzon tsira ya zo da shi ga dukkanin talikai.
Kamfanin dillancin labaran iqna ya habarta cewa ya nakalto daga shafin sadarwa na yanar gizo na ciyar bunkasa harkokin ilimi da al’adu cewa, mabiya addinin musulunci na kasar India sun gudanar da taron idul mab’as wato ranar aiko manzon Allah tsira da amincin Allah su tabbata a gare shi daiyalan gidansa tsarkaka da kuma muhimman darussan da ke cikin wannan sako mai tsari da manzon tsira ya zo da shi ga dukkanin talikai na duniya baki daya.
An habarta a shafin sadarwa na aynar gioz na FNC cewa an fara gudanar da wani zaman taro na majalisun dokoki na kasashen musulmi a birnin Dubai na kasar hadaddiyar daular larabawa wanda ke samun halartar wakilai daga kasashen musulmi da na larabawa daya daga cikin mambobi a kungiyar hadin kan kasashen musulmi.
A wani labarin kuma babban malamin addinin muslunci mai bayar da fatawa akasar Serbia ya tsaya takarar neman kujerar majalisar dokokin kasar a zabukan da za a gudanar a nan gaba da nufin zama mai wakiltar musulmi a majalisar dokin kasar ta Serbia wadda musulmi ne marassa rinjaye a cikinta.
Da dama daga cikin masana musulmi sun imanin cewa abubuwan da suka faru na cin zarafin musulmi da addinin muslunci a kasashen turai, da hakan ya hada da yada hotuna na zanen batunci ga manzon Allah tsira da amincin Allah ya tabbata a gare shi da iyalan gidansa tsarkaka, wata alama ce da ke nuni da cewa al’ummomin wadanan kasashen da ‘yan siyasarsu da shugabanninsu suna yin amfani da nuna adawa da musulunci da kuma yada kyamarsa atsakanin mutane a matsayin wata hanya ta neman matsayi na siyasa ko zamantakewa a cikin kasashen da suke gaba da musulmi da musulunci.
1034133