IQNA

Zaman Taro Na Ziyarar Ma’aiki (SAW) Tare Da Halartar Makaranta Kur’ani

17:11 - June 23, 2012
Lambar Labari: 2352584
Bangaren kasa da kasa, an gudanar da zaman taro na addu’ar ziyarar ma’aiki tsira da amincin Allah su tabbata a gare shi da iyalan gidansa tsarkaka a hubbaren manzon Allah da ke birnin Madina mai alfarma tare da halartar makaranta da mahardata kur’ani mai tsarki na kasashen ketare.
Kamfanin dilalncin labaran iqna ya habarta cewa ya nakalto daga shafin sadarwa na yanar gizo cewa, a jiya an gudanar da zaman taro na addu’ar ziyarar ma’aiki tsira da amincin Allah su tabbata a gare shi da iyalan gidansa tsarkaka a hubbaren manzon Allah da ke birnin Madina mai alfarma tare da halartar makaranta da mahardata kur’ani mai tsarki na kasashen ketare da suke gudanar da ziyara a ayyuakn umra.
ma’aikatar kula da harkokin muslunci ta kasar Syria ta sanar cewa ta dauki nauyin rubutawa tare da buga wani kwafin kur’ani mai tsarki mai tsarki wanda shi ne irinsa na farko a kasar da nufin kara fito da matsayin kur’ani a kasar wadda daya ce daga cikin kasashen musulmi da sukee taka gagarumar rawa wajen yada addinin musulunci.
Bayanin ya ci gab ada cewa wannan kur’ani na daga cikin muhimman ayyukan da wannan ma’aikata ta gudanar a cikin tarihinta, domin kuwa za a mayar da shi ta wata hanya da dukaknin muslumin kasar za su iya amfana da shi ta hanyoyi masu sauki, kamar saka shi a cikin na’urori na musamman da suke aiki da na’ura mai kwakwalwa, ta yadda za aiya karantawa da sauraren sauti.
Ma’aikatar kula da harkokin muslunci ta kasar Syria ta sanar cewa ta dauki nauyin rubutawa tare da buga wani kwafin kur’ani mai tsarki mai tsarki wanda shi ne irinsa na farko a kasar da nufin kara fito da matsayin kur’ani a kasar wadda a koda yaushe take kokaein ta samar da hanyoyin bunkasa fahimtar musulunci.
1035373


captcha