Kamfanin dilalncin labaran iqna ya habarta cewa ya nakalto daga shafin sadarwa na yanar gizo na Bernama cewa, yanzu haka gwamnatin kasar Malazia za ta kara karfafa harkokin saka hannayen jari a kasar bisa tsarin muslunci wanda aka fara tun kimanin shekaru hudu da suka gabata kuma yake ci gaba da samun karbuwa daga masu saka hannayen jari daga kasashen ketare a cikin kasar gami da kamfanoni na ciki da waje.
kalamai da shugaban majalisar dokokin kasar Lebanon ya yi a gaban baje kolin wasu hotuna da ke nuni da cin zarafin fararen hula da mahukuntan kasar Bahrain suke yi hakan ya harzuka sarakunan kama karya na kasar wadanda suke samun goyon baya daga sauran kawayensu ‘yan kama karya na tekun fasha.
Bayanin ya ci gaba da cewa, kasar Bahrain ta nuna maitar a fili tun daga lokacin da al’ummar kasar suka fara boren neman sauyi, da nufin tabbatar da adalci a tsakanin al’ummar kasar wadanda suke fuskantar zalunci da danniya tswon shekaru na tarihin kasar, amma abin da yafi komai ban mamaki shi ne yadda kasashen larabawa suka yi gum da bakunansu kan ta’asar da gwamnatin ta Bahrain take tafakawa.
Kalaman da Nabih Birri shugaban majalisar dokokin kasar Lebanon ya yi a gaban baje kolin wasu hotuna da ke nuni da cin zarafin fararen hula da mahukuntan kasar Bahrain suke yi hakan ya harzuka sarakunan kama karya na kasar wadanda suke samun goyon baya daga sauran kawayensu ‘yan kama karya na tekun fasha da suka shahara da kama karya a tarinsu.
1034127