Bangaren kasa da kasa, tsari da kuma yadda ake gudanar da gasar karatun kur’ani mai tsarki ta kasa da kasa a jamhuriyar muslunci ta Iran ya sha banbam da sauran yadda ake gudanar da irin wannan gasa a wannan matsayi a sauran kasashen musulmi.
A zantawar da ta hada shi da kamfanin dillancin labaran iqna a wajen taron gudanar da gasar karatu da hardar kur’ani mai tsarki a birnin Tehran karoo an ashirin da tara wakilin kasar Kuwait a wannan gasa Ali Ibrahim Askar ya bayyana cewa tsarin yadda ake gudanar da irin wannan gasa ajamhuriyar muslunci ta Iran ya sha banbam da sauran kasashe.
a karon farko za abude bankin muslunci a kasar Morocco wsanda zai fara aiki a cikin shekara mai kamawa da nufin karfafa ayyuka na tattalin arzikin kasar musamman ma ta fuskacin kasuwan da harkokin banki domin rage yawan korafin al’ummar kasar ta wannan fuska.
Banki dai yana ci gaba da samun karbuwa akasashen duniya da dama musamman kasashen larabawa da na musulmi, amma kuma alokaci guda wasu suna yin amfani da bankin ne domin manufofinsu na siyasa, kamar dai yadda muke gani a halin yanzu a kasar ta Morocco, inda kasar ba ta taba yin magana ko nuna sha’awarta kan wannan banki ba sai yanzu da take fuskanta matakla daga mutanen kasar.
Wannan dai shi ne karon farko za abude bankin muslunci a kasar Morocco wsanda zai fara aiki a cikin shekara mai kamawa da nufin karfafa ayyuka na tattalin arzikin kasar musamman ma ta fuskacin kasuwan da harkokin banki da sauran harkoki. 1034485