Bangaren siyasa da zamantakewa, mabiya addinin muslunci da suke zaune a tsibirin Bali na kasar Indonesia sun nuna rashin amincewarsu da wata doka da wasu makarntun yankin suka kafa ta hana saka hijibin musulunci ga mata masu karatu inda suka yi kira da a gaggauta janye wannan doka.
Kamfanin dillancin labaran iqna ya habarta cewa ya nakalto daga shafin sadarwa na yanar gizo na Angga Abimayu cewa mabiya addinin muslunci da suke zaune a tsibirin Bali na kasar Indonesia sun nuna rashin amincewarsu da wata doka da wasu makarntun yankin suka kafa ta hana saka hijibin musulunci ga mata masu karatu inda suka yi kira da a gaggauta janye wannan doka da suka kafa.
Shugaban cibiyar darul kur’ani na kasar Iraki ya sheda cewa a zantawarsa da iqna an fara gudanar da shirye-shirye na gidan radiyon kur’ani mai tsarki na garin Nasiriyya a kasar Iraki da nufin kara bunkasa dukaknin harkoki da suka danganci kur’ani da koyarwarsa a tsakanin al’ummar wannan kasa mai mai matukar muhimmanci a cikin kasashan musulmi.
A wani labarin kuma ministan harkokin cikin gidan kasar Jamus ya yi kakkausar suka kan mabiya tafarkin salafiyya dangane da abubuwan da suke yi a kasdar na wuce gona da iri da sunan cewa suna bin tafarkin addinin mulsunci ne da kuma rarraba kur’anai a tsakanin al’ummar kasar ta Jamus.
A bangare guda kuma ana shirin gudanar da wani shiri na musamman dangane da bayar da horo ga limaman masallatai na kasar Jamus, wanda jami’ar Snaburg ta kasar za ta dauki nauyin aiwatar da shi tare da hadin gwai da cibiyoyin mabiya addinin muslunci na kasar baki daya, wanda kuma ake ganin zai amfani matuka.
1036641