Kamfanin dillancin labaran iqna ya habarta cewa ya bakalto daga shafin sadarwa na yanar gizo cewa, an gudanar da tarukan makon al’adun kasar Iran a kasar Romania wanda ma’aikatar kula da harkokin al’adun muslunci ta kasar ta dauki nauyin shiryawa da gudanarwa wanda ya fara aiki tun daga farkon wannan mako da muke ciki.
An watsa labarai masu karo da juna dangane da makomar majalisar ministocin kasar masar karkashin jagorancin fira minitsna Kamal Janzuri wanda masu tsaurin ra’yin kishin islama suke tuhumarsa da kasawa yayin da majalisar sojin kasar ba ta ba shi goyon bayn da yake bukata wajen gudanar da ayyukansa na tafiyar da mulki.
Mambobin majasar dokokin kasar Masar sun yi kira da a safke babban malamin kasar mai bayar da fatawa bayan ya yi tafiya zuwa haramtacciyar kasar Isra’ila ba tare da izinin majalisa da kuma yin shawara da majalisar malaman addinin muslunci ta kasar ba lamarin da ake kallonsa a matsayin wani babban kure.
Tafiyar da Ali Juma’a ya yi zuwa birnin Qods ya yi ne tare da hadin gwiwa da ma’aikatar tsaro ta haramatcciyar kasar Isra’ila wanda kuma ko shakka babu hakan ya sanya gagarumin shakku a cikin zukatan mutanen kasar dangane da wannan ziyara tasa, duk kuwa da cewa daga cikin abubuwan da ya yi har da duba lafiyarsa a asibiti.
Yan majasar dokokin kasar Masar sun yi kira da a safke babban malamin kasar mai bayar da fatawa bayan ya yi tafiya zuwa haramtacciyar kasar Isra’ila ba tare da izinin majalisa da kuma yin shawara da majalisar malaman addinin muslunci ta kasar
1036761