IQNA

Mumunai Sun Gudanar Da Taron Maulidin Abbas (AS) A Birnin Makka Mai Alfarma

22:25 - June 25, 2012
Lambar Labari: 2354346
Bangaren kasa da kasa, An gudanar da taron maulidin Abul Fadl Abbas (AS) a birnin Makka tare da halrtar malaman addini da kuma mabiya tafarkin iyalan gidan amnzon Allah a dakin gudanar da taruka na babban otel din nan Murjanatul asil da ke birnin.
Kamfanin dilalncin labaran iqna ya habarta cewa ya nakalto daga shafin sadarwa na yanar gizo cewa, An gudanar da taron maulidin Abul Fadl Abbas (AS) a birnin Makka tare da halrtar malaman addini da kuma mabiya tafarkin iyalan gidan amnzon Allah a dakin gudanar da taruka na babban otel din nan Murjanatul asil da ke birnin mai alfarma.
Keta lafarmar kur’ani mai tsarki mummunan aiki ne da ya yi hannun riga da dukkanin dabiu na ‘yan adamtaka wanda kuma shi ne abin da duniya take ganin ana yi yanzua cikin kasashen yammacin turai da sunan ‘yancin fadar albarkacin baki ko bayyana ra’ayi bisa wannan dalilin suke cin karen su babu babbaka kan addinin muslunci.
wani dan majalisar dokokin kasar Algeria ya keta alfarmar kur’ani mai tsarki a cikin wata bababr kotu da ke birnin Aljerrs fadar mulkin kasar lamarin da ya bakanta ma daukacin al’ummar kasar inda ake yi kira da a gaggauta hukunta shi kan wannan babban laifi da ya aikata ba tare da wani bata lokaci ba.
A labari na daban kuma an habarta cewa jam’iyun adawa uku na masu kishin islama a kasar Algeria sun sanar da kafa wata babbar hadaka domin fuskantar zabuka masu a kasar da nufin kayar da jamiyya mai mulki a halin yanzu a kasar karkashin jagorancin shugaba Butaflika.
Wadannan jamiyu wadanda suka shafe tsawon lokaci suna adawa sun samu dama a wannan lokaci da ake bore a cikin wasu kasashen larabawa domin kawar da gwamnatoci ‘yan kama karya da suke yin amshin shata ga Amurka, misali daga ciki kuwa shi ne abin da ya faru akasar Masar, inda aka kawar da tsohon shugaban mulkin kama karya dan koren Amurka, kuma masu kishin islama suka mamaye sha’anin mulki.
1036433




captcha