Kamfanin dillancin labarai na ikna da ke kula da harkokin da suka shafi kur'ani mai girma a nan jamhuriyar musulunci tai ran ne ya watsa rahoton cewa: hardar kur'ani dole ta yi daidai da tunani da ke cikin ayoyin kuma a ga haka a cikin rayuwa da ayyukan yau da kullum na mahardata kur'ani mai girma ta inda ayoyin kur'ani za su saje da rayuwa da tunanin mahardatan.Abdulkadir Jalu mahardacin kur'ani mai girma daga kasar Seraleyon da ya halarci gasar karatun gasar kur'ani mai girma ta kasa da kasa karo na ashirin da tara da aka gudanar a nan jamhuriyar musulunci tai ran da cewa : burina na hardar kur'ani mai girma shi ne sanin wani abu daga maganar Allah da kuma kasancewa tare da kur'ani mai girma.
1037442