Bangaren kasa da kasa, za a gudanar da sallolin khatama ga ma’asumai goma sha hudu a birnin Makka mai alfarma wanda daliban karatun kur’ani mai tsarki da suka isa birnin daga jamhuriyar muslunci ta Iran za su gudanar a dakin gudanar da taruka Murjanah da ke birnin.
Kamfanin dilalncin labaran iqna ya habarta cewa ya nakalto daga shafin sadarwa na yanar gizo cewa, za a gudanar da sallolin khatama ga ma’asumai goma sha hudu a birnin Makka mai alfarma wanda daliban karatun kur’ani mai tsarki da suka isa birnin daga jamhuriyar muslunci ta Iran za su gudanar a dakin gudanar da taruka Murjanah da ke birnin kamar dai yadda aka saba yi a kowace shekara.
A wannan karon an mayar da gasar karatun kur’ani gami da harda da aka gudanar a matsayi na kasa da kasa a birnin Tehran karo na 29 zuwa matakai uku wanda kuma hakan ne ya kara fito da gasar fiye da sauran shekarun baya kamar yadda mahalarta daga kasashen ketare suka bayyana ga manem alabarai.
Wannan dai shi ne karo na 29 da ake gudanar da gasar karatun kur’ani mai tsarki a birnin Tehran a kowace shekara da nufin kara daukaka matsayin kur’ani ga sauran al’ummomin duniya sanin irin sako mai tsarki da yake da shi ga al’ummomin duniya, wanda manzon tsira annabin rahma tsira da amincin Allah su tabbata a gare shi da iyalan gidansa tsarkaka ya zo da shi.
A wannan karon an mayar da gasar karatun kur’ani gami da harda da aka gudanar a matsayi na kasa da kasa a birnin Tehran karo na 29 zuwa matakai uku wanda kuma hakan ne ya kara fito da gasar fiye da sauran shekarun baya kamar yadda mahalarta daga kasashen ketare suka bayyana masu daukar labarai na kamfanin dilalncin labaran kur’ani mai tsaki na iqna a wajen taron. 1038943