Kamfanin dilalncin labaran iqna ya habarta cewa ya nakalto daga shafin sadarwa na yanar gizo na Nun cewa, an gudanar da wani zaman taro mai taken Imam Hussain (AS) da ranar Ashura a birnin karbaka mai alfarma a daidai lokacin da ake gudanar da tarukan watan sha’aban mai albarka tare da halartar baki ‘yan kasashen ketare.
Bayanin ya ci gaba da cewa yanzu haka dai an samar da hanyar gane abincin halal a kasar Faransa ta hanyar yin amfani da na’ura mai kwakwalwa da za a iya yin amfani da ita ta hanyar wayar salula da ake kira just halal wadda nan ba da jimawa za a fara sayar da ita a kasuwa domin amfanin musulmi da ma masu shaawar hakan bisa la’akari da cewa akwai wadanda ba musulmi ba amma suna amfana da hakan.
A wani labarin kuma wasu masu zanga-zanga sun kone tutocin haramtacciyar kasar Isra’ila da uwar gijyarta Amurka a kasar turkiya domin nuna fushi kan kiesan gillan da da suke yi kan al’ummar musulmi a cikin palastinu da kuma kasar Afghanistan a cikin lokutannan saboda tsabar zalunci da danniya kan musulmi.
Masu zanga-zangar a cikin fushi sun banzama kan m,anyan tituna acikin birane da dama da suka hada da birnin Istanbul babbar cibiyar kasuwancin kasar ta Turkiya, kamar yadda aka gudanar da wata gagarumar zanga-zangar irin wannan a cikin birnin Ankara fadar mulkin kasar ta siyasa.
1038869