Bangaren kasa da kasa: hadin gambizar kungiyoyin addini a Latin Amerika sun fitar da wani bayani da a cikinsa suna sanar da fara azumin bana a kasashen Arewacin Amerika a ranar juma'a talatin daidai ga watan Tir na shekara ta dubu daya da dari uku da tis'in hijira shamsiya a matsayin ranar farko ta watan azumin wannan shekara ta dubu daya da dari hudu da talatin da uku hijira kamariya.
Kamfanin dillancin labarai na ikna da ke kula da harkokin da suka shafi kur'ani mai girma a nan jamhuriyar musulunci ta Iran ne ya watsa rahoton cewa; hadin gambizar kungiyoyin addini a Latin Amerika sun fitar da wani bayani da a cikinsa suna sanar da fara azumin bana a kasashen Arewacin Amerika a ranar juma'a talatin daidai ga watan Tir na shekara ta dubu daya da dari uku da tis'in hijira shamsiya a matsayin ranar farko ta watan azumin wannan shekara ta dubu daya da dari hudu da talatin da uku hijira kamariya.Majiyar labarai ta Safir News ne ta watsa labarin cewa:karkashin wani lissafi da malaman addini na kasashen Latine Amerika suka yi ne suka tamtance da fara azumin bana a yankin a ranar talatin ga watan Tir na wannan shekara a matsin ranar farko ta watan azumi yayin da kuma za a kammala shi a ranar ashirin da takwas ga watan Murdad na shekara ta dubu daya da dari uku da tis'in da daya hijira shamsiya kuma za su yi sallar babbar salla a ranar ashirin da tara ga watan na Murdad na wannan shekara .kuma dama haka al'ummar yankin suka saba suna fara azumin ne a kowace shekara karkashin fatawa daga wannan komiti day a hada malamai addini a wannan yanki na arewacin Amerika wato kasashen Latin Amerika. Da fatar das u al'ummomin yanki da sauran musulmin duniya za su yi azumin bana cikin kwanciyar hankali da nucuwa.
1039524