Bangaren kasa da kasa;Kungiyar gwagwarmaya ta Hizbulllah a kasar Labanon da kuma wasu kungiyoyin Palasdinu da ke zaune a kasar ta Labanon sun fitar da wani bayani na hadin guiwa da a ciki suke yin Allah wadai da yadda hukumomi na kasa da kasa da kungiyoyin kasa da kasa suka yi gum da bakinsu na klubalantar mummunan siyasar nuna kama da danne dan adam da haramtacciyar kasar isra'ila ke nunawa al'ummar Palasdinu.
Kamfanin dillancin labarai na ikna da ke kula da harkokin da suka shafi kur'ani mai girma a nan jamhuriyar musulunci ta Iran ne ya watsa rahoton cewa; Kungiyar gwagwarmaya ta Hizbulllah a kasar Labanon da kuma wasu kungiyoyin Palasdinu da ke zaune a kasar ta Labanon sun fitar da wani bayani na hadin guiwa da a ciki suke yin Allah wadai da yadda hukumomi na kasa da kasa da kungiyoyin kasa da kasa suka yi gum da bakinsu na klubalantar mummunan siyasar nuna kama da danne dan adam da haramtacciyar kasar isra'ila ke nunawa al'ummar Palasdinu.A ranar shidda ga watan tir na shekara ta dubu daya da dari uku da tis'in da daya a wani taron hadin guiwa da suka yi a tsaklaninsu day a hada mambobin kungiyar gwagwarmaya ta Hizbullahi da kuma wasu kungiyoyin na Palsdinawa da suke zaune a kasar ta Labanon sun yi Allah wadai da yadda hukumomin kasada kasa da kungiyoyin kasa da kasar suka yi gum da bakinsu bas u cewa komi kan duk wani ta'addanci da babakere da gwamnatin Haramtacciyar kasar Isra'ila ke nunawa kan fararen hula Palasdinawa kuma bayan wannan Allah wadai da suka yi sun kuma yi kira da abbbara murya da al'ummomi na duniya da hukumomi msu lamiri da kungiyoyi da su yi wani yunkuri na ganin an kawo karshen wannan cin kasha da ake nunawa al'ummar Palsdinu.
1039249