IQNA

An Gudsanar Da Babban Zaman taro Tsakanin Kasashen Musulmi Da China

0:45 - July 01, 2012
Lambar Labari: 2357618
Bangaren kasa da kasa, ana ci gaba da gudanar da taro tsakanin kasashen musulmi da kuma kasar China abirnin Beijin fadar mulkin kasar tare da halartar wakilai na kasshen musulmi da kuma masana daga wasu kasashen musulmi da na larabawa da kuma wakilan gwamnatin China.
Kamfanin dillancin labaran iqna ya habarta cewa ya nakalto daga shafin sadarwa na yanar gizo cewa ana ci gaba da gudanar da taro tsakanin kasashen musulmi da kuma kasar China abirnin Beijin fadar mulkin kasar tare da halartar wakilai na kasshen musulmi da kuma masana daga wasu kasashen musulmi da na larabawa da kuma wakilan gwamnatin China wanda ke gudana yanzu haka har tsawon mako guda.
A bangare guda kuma gwamnatin kasar China zata jagoranci tattaunawa tsakanin kasashe biyar na farko wadanda suka mallaki makaman nuclear a duniya, inda ko wace kasa daga cikin kasashen biyar zata bada haske dangane da makaman nuclear da ta mallaka da kuma abinda ya shafi shirinta na nuclear.
Majiyar kasashen biyar ta bayyana a jiya jumma'a cewa wannan dai shi ne karo na farko wanda kasar China, wacce tafi ko wanne daga cikin sauran kasashen biyar boye batun shirinta na nuclear, zata jagoranci irin wannan zaman.
A cikin fasalin bazara da muke ciki ne ake saran wakilan kasashen China, Amurka, Britani, Faransa da kuma Rasha zasu bude tattaunawa kan makaman nuclearsu, da bayyana yawan makaman da kowannensu ya mallaka da kuma mai yuwa yerjejeniyar kwance damararsu.
Bisa kididdigan wasu kungiyoyin kayyade makamai a duniya dai kasar Amurka ta na da makaman Nuclear kimani 5000, kuma ita ce kadai ta taba amfani da su a kan mutane, sai kuma kasar Rasha wacce ta mallaki makaman nuclear 5500, a yayin da kasashe Faransa, Britani da kuma China suke da mallaki makaman 300, 225 da kuma 240 a jere.
1040508
captcha