IQNA

Kimanin Malaman Addini 2100 Ne Suke wayar Da Kan Maniyata A Turkiya

21:11 - June 30, 2012
Lambar Labari: 2357622
Bangaren siyasa da zamantakewa, malaman addinin muslunci dubu buyu da dari daya ne suke gudanar da taruka na wayar da kan maniyyata na wannan shekara asassa na kasar Turkiya tare da gabatar da laccoci da bayanai da kasidu da kuma makaloli da suke bayani kan wannan ibada mai girma.
Kmafanin dillancin labaran iqna ya nakalto daga shafin sadarwa na yanar gizo na Hasan Kamil cewa, sama da malaman addinin muslunci dubu buyu da dari daya ne suke gudanar da taruka na wayar da kan maniyyata na wannan shekara asassa na kasar Turkiya tare da gabatar da laccoci da bayanai da kasidu da kuma makaloli da suke bayani kan wannan ibada mai girma da matsayi na musammana wajen Allah madaukakin sarki.
Da dama daga cikin masana musulmi sun imanin cewa abubuwan da suka faru na cin zarafin musulmi da addinin muslunci a kasashen turai, da hakan ya hada da yada hotuna na zanen batunci ga manzon Allah tsira da amincin Allah ya tabbata a gare shi da iyalan gidansa tsarkaka, wata alama ce da ke nuni da cewa al’ummomin wadanan kasashen da ‘yan siyasarsu da shugabanninsu suna yin amfani da nuna adawa da musulunci da kuma yada kyamarsa atsakanin mutane a matsayin wata hanya ta neman matsayi na siyasa ko zamantakewa a cikin kasashen da suke gaba da musulmi da musulunci.
Har ila daga cikin irin wadannan munanan ayyukan da irin wadannan mutane suke aiwatarwa a kasashen yammacin turai har da sanar da ranar kone kur’ani ta duniya da wani la’antacen mutum ya yi a kasar Amurka ba tare da an ce masa uffan ba, da kuma zanga-zangar da wasu mutane suka yi akasar Jamus ta gaba da musulunci, daga karshe-karshen nan kuma sojojin Amurka sun banka wuta kan kur’ani mai tsarki a kasar Afghanistan.
1040529



captcha