IQNA

Wani Labari Da Ba Tabbatar Ba Ya Ambaci Mutuwar Sarkin Saudiyya

21:15 - June 30, 2012
Lambar Labari: 2357623
Bangaren kasa da kasa, wasu shafuka na yanar gizo na cikin kasar Saudiyya sun bayar da labarin mutuwar sarkin kasar Abdullah Bin Abduaziz wanda ke fama da matsananciyar rashin lafiya bayan mutuwar yarima mai jiran gado da bai wuce watanni takwas da nada shi kan wannan matsayi ba.
Kamfain dilalncin labaran iqna ya nakalto daga shafin sadarwa na tashar rasid cewa, yanzu haka dai wasu shafuka na yanar gizo na cikin kasar Saudiyya sun bayar da labarin mutuwar sarkin kasar Abdullah Bin Abduaziz wanda ke fama da matsananciyar rashin lafiya bayan mutuwar yarima mai jiran gado da bai wuce watanni takwas da nada shi kan wannan matsayi ba wanda shi ma ba san makomarsa, amma dai jami’an tsaro na ci gaba da bazuwa koina acikin birnin Riyad da wasu birane.
A wani labarin na daban kuma dubban daruruwan mutane sun gudanar da zanga-zangar nuna goyon baya ga al’ummar kasar Bahrain a kasar Iraki, saboda tsabar zaluncin da suke fuskanta daga masarautar kama karya ta kasar, inda ake murkushe su da karfi tare da kame su da azabtar da su saboda sun nemi hakkokinsu na ‘yan kasa da aka haramta musu.
A kwanakin baya ne dai bayan watsa wani labari da ke cewa masarautar kasar Bahrain na shirin kama shugaban majalisar malaman addinin muslunci ta kasar Ayatollah Sheikh Isa Kasim majalisar ta ja kunnen masarautar da ta shiga taitayinta dangane da duk wani mataki da za ta dauka kan wannan bakar aniya.
Wanann mataki da masarautar kasar Bahrain ke neman dauka kan shehin malami baya rasa nasaba da irin kiran da yake yi ne ga mahukuntan da su saurari bukatun mutane domin warware takaddamar da ake fama da ita, maimakon yin amfani da karfin tuwo wajen murkushe fararen hula masu neman hakkokinsu da aka haramta musu.
Bayan watsa wani labari da ke cewa masarautar kasar Bahrain na shirin kama shugaban majalisar malaman addinin muslunci ta kasar Ayatollah Sheikh Isa Kasim majalisar ta ja kunnen masarautar da ta kwana da sanin cewa, duk abin da ya samu malamin to zai kare a kanta ne.
Mutanen Bahrain dai kamar sauran al’ummomin larabawa suna neman hakkokinsu ne da aka haramta musu ta hanyar lumana, amma mahukuntan kasar tare da na kasar Saudiyya da kuma taimakon Amurka da Birtaniya.
1040597





captcha