IQNA

An Zargi Haramtacciyar Kasar Isra’ila Da Kashe Kusa A Kungiyar Hamas

21:14 - June 30, 2012
Lambar Labari: 2357624
Bangaren kasa da kasa, ma’aikatar harkokin cikin gida a yankin Gaza ta zargi haramtacciyar kasar Isra’ila da hannu kai tsaye wajen kisan gilla a kan wani kusa na kungiyar a birnin Damascus na kasar Syria bayan da wasu daga cikin masu yi ma haramtacciyar gwamnatin yahudawan suka furta cewa lallai wannan aikinsu ne.
Kamfanin dilalncin labaran iqna ya habarta cewa ya nakalto daga shafin sadarwa na yanar gizo cewa, ma’aikatar harkokin cikin gida a yankin Gaza ta zargi haramtacciyar kasar Isra’ila da hannu kai tsaye wajen kisan gilla a kan wani kusa na kungiyar a birnin Damascus na kasar Syria bayan da wasu daga cikin masu yi ma haramtacciyar gwamnatin yahudawan suka furta cewa lallai wannan aikinsu ne kuma an shirya hakan ne bayan samun damar bazuwar rikici a cikin kasar Syria.
Wani mamba a majalisar dokokin haramtacciyar kasar Isra’ila ya yi kakkausar suka dangane nuna wariya da da take yi tsakanin mutanen da suke cikin yankunan palastinawa da ta mamaye musamman ga larabawa mazauna yankunan da ake kira da Isar’ila a halin yanzu.
Ma'aikatar tsaron cikin gida da tattaro bayanan sirri ta kasar Iran ta sake fitar da sabbin bayanai dangane da nasarar da ta samu na gano 'yan wata kungiyar leken asiri da ke aiki wa HKI a cikin kasar da kuma gudanar da ayyukan ta'addanci da kisan gilla.
A cikin wata sanarwa da ma'aikatar ta fitar ta bayyana cewar jami'anta sun sami nasarar kame mutane 15 da suka hada da wasu 'yan kasar Iran da kuma wasu 'yan kasashen waje da suke aiki wa kungiyar leken asirin HKI (MOSSAD) a cikin Iran kuma tuni sun amince da wannan zargi da ake musu bayan da aka gabatar musu da hujjojin da suke tabbatar da hakan.
Har ila yau cikin wannan sanarwar ma'aikatar tsaron kasa da tattaro bayanan sirri ta Iran ta ce daga cikin ayyukan da aka ba wa wadannan 'yan leken asiri har da kashe daya daga cikin masanan kasar, to sai dai kuma sakamakon himmar jami'an tsaron kasar Iran din sun sami nasarar kawar da wannan makircin.
Haka nan kuma ma'aikatar ta ce wasu ayyukan da 'yan wannan kungiyar suke shirin aiwatarwa kafin a kama su din sun hada har da sanya bama-bamai a wasu wajaje masu muhimmanci, ayyukan ta'addanci da kuma kai hari a lokacin jerin gwano tunawa da ranar da juyin juya halin Musulunci ya yi nasara a kasar Iran da aka gudanar a watannin baya.

1040532





captcha