IQNA

Tarihin Rayuwar Imam Da Jagoran Jamhuriyar Musulunci Ta Iran A Aikace A Labanon

Bangaren siyasa da zamnatakewa; ofishin da ke kula da harkokin da suka shafi yada al'adun jamhuriyar musulunci ta Iran a kasar Labanon tare da hadin guiwar Talbijin din Alsirat sun fara nuna wani jerin shiri na talbijin da aka bashi taken sharfi kan rayuwar Imam Khomeini ® muassasin jamhuriyar musulunci ta Iran da kuma Ali Khamna'I jagoran juyin juya halin musulunci ta Iran kuma wannan shiri na talbijin an shirya shi ne a cikin harshen larabci.



Kamfanin dillancin labarai na ikna da ke kula da harkokin da suka shafi kur'ani mai girma a nan jamhuriyar musulunci ta Iran ne ya watsa rahoton cewa; ofishin da ke kula da harkokin da suka shafi yada al'adun jamhuriyar musulunci ta Iran a kasar Labanon tare da hadin guiwar Talbijin din Alsirat sun fara nuna wani jerin shiri na talbijin da aka bashi taken sharfi kan rayuwar Imam Khomeini ® muassasin jamhuriyar musulunci ta Iran da kuma Ali Khamna'I jagoran juyin juya halin musulunci ta Iran kuma wannan shiri na talbijin an shirya shi ne a cikin harshen larabci. Yazuwa yanzu an watsa shirye shirye guda tara kuma an fara watsa su ne tun cikin watan rajab na shekara ta dubu daya da dari uku da tis'in hijira kamariya ta dubu daya dari hudu da talatin da uku kuma mutane da dama sun nuna gamsuwarsu da wannan shiri da yadda suka karu kan abubuwa da daman a ilimi da yadda rayuwar wadannan bayun Allah ke kumshe da abubuwa da ilimi da fadakarwa da kuma amfani ga duk wani mai son yin rayuwa mai sauki da kusantar Allah madaukakin sarki. Har ila yau an tabo wani bangaren na rayuwarsu ta gwagwarmaya da taimakawa maras galihu da kokarin kubutar da duk wani da ake zalunta a wannan duniya.
1040600