IQNA

Musulunci Ya Zama Wani Bangare Na Rayuwar Mutanan Jamus

Bangaren kasa da kasa; shekaru biyu da suka gabata lokacin da Karistine Welf shugaban kasar Jamus na wannan lokaci ya bayyana cewa: addinin musulunci wani bangare ne na rayuwar al'ummar kasar Jamus ya fuskanci suka da maida martini daga masu tsananin ra'ayi da riko da demokradiya da ra'ayin kiristanci a kasar Ta Jamus.




Kamfanin dillancin labarai na ikna da ke kula da harkokin da suka shafi kur'ani mai girma a nan jamhuriyar musulunci ta Iran ne ya watsa rahoton cewa; shekaru biyu da suka gabata lokacin da Karistine Welf shugaban kasar Jamus na wannan lokaci ya bayyana cewa: addinin musulunci wani bangare ne na rayuwar al'ummar kasar Jamus ya fuskanci suka da maida martini daga masu tsananin ra'ayi da riko da demokradiya da ra'ayin kiristanci a kasar Ta Jamus. To shi ma sabon shugaban kasar ta Jamus YuAkhim Gauk a kokarinsa na bayyana hakika da kare shugaban day a gada kan wannan Magana ta gaskiya da dattako day a nuna ya bayyana cewa; musulmi wani bangare ne na al'ummar kasar Jamus amma ba musulunci ba . To wannan magana tasa shi abin da masu iya Magana kan ce ba cinya b ace kafar baya ce domin mane ne banbancin musulmi da kuma musulunci idan za a kalli abin ta mahangar zamantakewar al'umma domin idan aka amince da kasancewar musulmi da kare musu hakkinsu dole a yarda da matsayin addinin musulunci an ki ko an so. Kua a yau kimanin musulmi miliyon hudu ne ke rayuwa kuma yan kasar ta jamus kuma dokokin kasar ya bas u damar da yancin rayuwa da yancin gudanar da lamuran addininsu babu wata tsangwama da takurawa to ta yaya ne za a raba addinin musulunci da rayuwar al'ummar Jamus? To amsasr wannan Magana a fili take ko shakka babu.Idan aka waiwaya a baya a shekarun da suka shige za a ga yawan musulmi a wannan kasar karuwa yake yi a kowace shekara misali a shekara ta dubu daya da dari tara da arba'in da biyar bayan kawo karshen yakin duniya na biyu musulmi dubu shida ne kacal ke rayuwa a kasar ta Jamus amma yau kimanin miliyan hudu .
1039873