IQNA

Iraniyawa Mazauna Faransa Za Su Raya Nisfis Shaaban

15:06 - July 01, 2012
Lambar Labari: 2358377
Bangaren kasa da kasa: Iraniyawa da ke zaune a kasar Faransa za su halarci wani buki na tunawa da zagayowar ranar haifuwar Imam Mahdi (Aj) ranar nisful Sha'aban na shekarar bana ta dubu daya da dari hudu da talatin da uku da za a gudanar a ranar sha hudu da watan Tir na shekara ta dubu daya da dari uku da tis'in da daya hijira shamsiya kuma a birnin Paris babban birnin kasar Faransa ne za a gudanar da wanna bukin .


Kamfanin dillancin labarai na ikna da ke kula da harkokin da suka shafi kur'ani mai girma a nan jamhuriyar musulunci ta Iran ne ya watsa rahoton cewa; Iraniyawa da ke zaune a kasar Faransa za su halarci wani buki na tunawa da zagayowar ranar haifuwar Imam Mahdi (Aj) ranar nisful Sha'aban na shekarar bana ta dubu daya da dari hudu da talatin da uku da za a gudanar a ranar sha hudu da watan Tir na shekara ta dubu daya da dari uku da tis'in da daya hijira shamsiya kuma a birnin Paris babban birnin kasar Faransa ne za a gudanar da wanna bukin . A wannan daren za a gudanar da bukin ne da misalign karfe shida zuwa takwas na daren kuma ofishin da ke kula da yada al'adun jamhuriyar musulunci ta Iran a wannan kasar ne ya shirya inda malamai na jami'a da malaman addini da nazarta za su gabatar da jawabai da kuma waken yabon Imam Mahdi (AJ).

1040831
captcha