IQNA

Musulmin Kasar faransa Sun Haramta Coca-cola Da Pepsi Saboda wasu dalilai

15:53 - July 01, 2012
Lambar Labari: 2358439
Bangaren kasa da kasa, mabiya addinin muslunci a kasar faransa sun haramta sha nauoin lemun kwalba na coca cola da kuma pepsi bisa hujjar cewa an samu wani sakamakon bincike da ya yi nuni da cewa akwai wani kaso kadan matuka na alkahol a cikinsu wanda kuma ya samu ne sakamon sarrafa ma’adanan da ake amfani da su wajen yin lemun.
Kma,fanin dilalncin labaran iqna ya habarta cewa ya nakalto daga shafin sadarwa na yanar gizo na algerie-fosus cewa mabiya addinin muslunci a kasar faransa sun haramta sha nauoin lemun kwalba na coca cola da kuma pepsi bisa hujjar cewa an samu wani sakamakon bincike da ya yi nuni da cewa akwai wani kaso kadan matuka na alkahol a cikinsu wanda kuma ya samu ne sakamon sarrafa ma’adanan da ake amfani da su wajen yin lemun wanda ba an saka shi be bisa niyya.
Na ba da jimawa ba za a gudanar da wani baje koli na kayan abinci na halal a birnin paris na kasar faransa tare da hadin gwiwa da cibiyoyin mabiya addinin muslunci wadanda suke da dangantaka da kamfanonin kasar da suke samar da ababen bukata bisa yarjejeniya a tsakaninsu da wadannankamfanoni, inda a halin yanzu za su kawo kaya na ahalal bisa yarjejeniyar kamfanoni.
Wannan baje kolin zai nuna irin kayan da ake samarwa a kasashen muslmi da suke samar da kayan abincin halal kuma suke fitar da su zuwa kasashen ketare, daga ciki kuwa har da kamfanonin kasashen malazia da Indonesia gami da wasu daga cikin kasashen musulmi da na larabawa, baje kolin zai taimaka matuka wajen banbance kayayyakin a tsakanin sauran kayan abinci da ake sayarwa a shaguda da kwasunnin kasar ta Faransa da ke musulmi masu tarin yawa.
Masana sun yi imanin cewa gudanar da wannan baje koli na kayan abinci na halal a birnin paris na kasar faransa tare da hadin gwiwa da cibiyoyin mabiya addinin muslunci wadanda suke da dangantaka da kamfanonin kasar da suke samar da ababen bukata bisa yarjejeniya a tsakaninsu yana da matukar muhimmanci ga musulmi da ma masu bukatar cin abin halal na musulmi.
1040907


captcha