IQNA

Gadon Sarauta Ya Girgiza Kasar saudiya Sakamakon Rashin lafiyar sarki

20:14 - July 02, 2012
Lambar Labari: 2359465
Bangaren kasa da kasa, abubuwan da suke faruwa na neman mulki a cikin gidan sarautar Ali-saud na ci gaba da kara muni bayan da sarkin kasar ya shiga wani yanayi na rashin lafiya mai tsanani da kuma mutuwar da masu jiran gado na kasar ke a cikin lokutan nan.
Kamfanin dilalncin labaran iqna ya habarta cewa ya nakalto daga shafin sadarwa na yanar gizo cewa, , abubuwan da suke faruwa na neman mulki a cikin gidan sarautar Ali-saud na ci gaba da kara muni bayan da sarkin kasar ya shiga wani yanayi na rashin lafiya mai tsanani da kuma mutuwar da masu jiran gado na kasar ke a cikin lokutan nan inda yarima biyu suka mutu cikin kasa da watanni takwas.
Majiyar gwamnatin kasar Saudiyya ta karyata labarin mutuwar sarkin kasar Abdullahi bin Abdul-Aziz dan shekaru 88 a duniya.
Majiyar ta bayyana cewar labaran da wasu kafafen watsa labarai suka watsa na mutuwar sarkin Saudiyya Abdullahi bin Abdul-Aziz labari ne maras tushe da baya da wani inganci. Majiyar ta kara da cewa; a kwanakin baya an kwantar da sarkin na Saudiyya a wani asibitin birnin Riyadh fadar mulkin kasar sakamakon matsalar hawan jini, amma a halin yanzu baya fuskantar wata barazana ta lafiya.
Wasu kafofin watsa labarai musamman na Larabawa sun sanar da mutuwar sarki Abdullahi bin Abdul-Aziz dan shekaru 88 a duniya a wajen shakatawarsa da ke kasar Moroko, lamarin da ya sanya daukan tsauraran matakan tsaro na musamman a duk fadin kasar ta Saudiyya.
1042075






captcha