IQNA

Jiran Bayyanar Hujjar Allah A Bayan Kasa Shi Ne Hakikanin Jira Na Fadakar Duniya

Bangaren fikira, jiran bayyanar hujjar Allah madaukakin sarki a bayan kasa shi ne hakikanin jira na bayyanar fadakar musulmin duniya karkashin jagoranmcin limami da Allah ya wajabta yin biyayya gare shi bisa umurninsa wanda hakan ne kuma zai kai ga dan adam zuwa ga hakikanin shiriya da fadaka.
Kamfanin dilalncin labaran iqna ya habarta cewa ya nakalto daga shafin sadarwa na yanar gizo cewa, mataimakin shugfaban cibiyar ilimi ta Hauza, ya bayyana cewa jiran bayyanar hujjar Allah madaukakin sarki a bayan kasa shi ne hakikanin jira na bayyanar fadakar musulmin duniya karkashin jagoranmcin limami da Allah ya wajabta yin biyayya gare shi bisa umurninsa wanda hakan ne kuma zai kai ga dan adam zuwa ga hakikanin shiriya da fadaka wadda babu wani shakku a cikinta.
Majalisar mabiya addinin muslunci a kasar Faransa za ta shigar da kara kan mutanen da suek nuna matuar adawa da addinin muslunci a kasar faransa saboda abin da suke yi na kokarin haddasa rikici da rashin fahimtar juna tsakanin mabiya addinin musulunci da sauran mabiya addainai da suke zaune a kasar.
Bayanin ya ci gaba da cewa kasar Faransa na daga cikin kasashen nahiyar turai da suka fi yawan musulmi, ta yadda adadinsu ya zama su ne na biyu ta fuskacin yawa a kasar bayan mabiya addinin kiristanci, amma kuma duk da haka har yanzu gwamnatin kasar ba ta amince da addinin musulunci a hkumance ba amatsayin daya daga cikin addinain kasar, duk kuwea da cewa ta amince da addinin yahudanci.
1043205