Kamfanin dillancin labarai na Ikna da ke kula da harkokin da suka shafi kur'ani mai tsarki a nan jamhuriyar musulunci ta Iran ne ya watsa rahoton cewa: Muhammad Mursi sabon shugaban kasar Masar sau tari ya ki amsa wayar tarhon domin tattaunawa da Natanyahu firaministan Haramtacciyar kasar Isra'ila.Majiyar labarai ta CPI ne ta watsa labarin cewa: Muhammad Mursi sabon shugaban kasar Masar ya ki amsa buga wayar da firaministan haramtacciyar kasar Isra'ila Natanyahu yayi masau sau da dama kuma yana son taya kungiyar ta Ikhwanul muslim wannan nasar da ta samu inda dan takararta ya zama sabon shugaban kasar Masar a cikin tarihi na zaben da aka gudanar ta hanyar demokradiya da kuma zaben farko day a biyo bayan boren da al'ummar kasar ta yin a Koran dan kama karya da mulkin danniya na tsawon shekaro a kasar wato Husni Mubarak.Hat firaministan na Haramtacciyar kasar Isara'ila bayan ya yi kokarin ganin sabon shugaban na kasar Masar ya amsa masa wannan tambaya tasa ya bukaci shugaban kasar Amerika Barak Obama day a sa baki ya masa masa wannan waya amma bai kai ga cin nasara ba.
1043210