IQNA

Lokacin Tsoron Gwamnatin HKI Ga Kasar Masar Ya Kawar

14:48 - July 04, 2012
Lambar Labari: 2361150
Bangaren kasa da kasa;Muhammad Albaltaji sakataren jam'iyar yanci da adalci da ke bangare ne na kungiyar siyasa na jama'atul Ikhwanul musulim a kasar masar ya bayyana cewa: gwamnatin haramtacciyar kasar Isra'ila dole ta sani cewa lokacin fargaba da tsoron da kasar Masar ta ke yi mata ya kawar.



Kamfanin dillancin labarai na Ikna da ke kula da harkokin da suka shafi kur'ani mai girma a nan jamhuriyar musulunci ta Iran ne ya watsa rahoton cewa: Muhammad Albaltaji sakataren jam'iyar yanci da adalci da ke bangare ne na kungiyar siyasa na jama'atul Ikhwanul musulim a kasar masar ya bayyana cewa: gwamnatin haramtacciyar kasar Isra'ila dole ta sani cewa lokacin fargaba da tsoron da kasar Masar ta ke yi mata ya kawar.An nakalto daga majiyar labarai ta Almanar cewa: sakataren jam'iyar yanci da adalci gwamnatin kasar Masar bat a neman tashin hankali da yanayi na dar dark o tashin hankali da wata kungiya ko gwamnati amma a daidai lokacin guda sabuwar gwamnatin kasar Masar ba kwanwar lasa b ace duk wanda ya hauta sai y arena kansa kuma za ta iya jurewa duk wani matsin lamba sai ta cimma abin da ta sanya a gaba. Ya kara da cewa; shiga da fita ba tare da neman iznin shiga a yankin hamadar Sina da mambobin gwamnatin Haramtacciyar kasar Isra'ila ke yi yana daya daga cikin abubuwan da za a sake yin dubi a cikinsa kuma ci gaba da barin wannan yanayi yana wanzuwa na barazana ga kasar Masar.
1043999



captcha