Kamfanin dillancin labarai na Ikna da ke kula da harkokin da suka shafi kur'ani mai girma a nan jamhuriyar musulunci ta Iran ne ya watsa rahoton cewa: yan shi'a a garuruwa daban daban da biranai na Tarayyar Nigeria za su gudanar da tarurruka da daman a tunawa da irin wannan rana ta zagayowar ranar Haifuwar Imam Mahdi Imam Asr (AJ).Irin buki da taron addini an saba gabatar das hi a fadin Nigeria kuma yana daga cikin muhimman guraren gudanar da taron addini mafi kayatarwa a tsakanin kasashen afrika kuma a wannan karon Harakar musulunci mmu'assisar Kausar da mu'assisar sakalain ne za su gudanar da halartar yan uwa mata da maza a garuruwa daban daban kamar Kaduna,Zariya, kano,Katsina,Yola da bauchi. Har ila yau malamai da masana addini za su gudanar da jawabai kan wannan rana mai muhimmanci.
1043743