Bangaren kasa da kasa; duk da cewa kimanin kaso daya cikin dari na al'ummar Amerika musulmi ne amma duk da haka kaso sha uku cikin dari na musulmin Amerika ke fuskantar muzgunawa da takurawa misali a shekarar da ta gaba ta kawai an samu karuwar masu takuwa musulmi da masu tsananin nuna adawa da karan zuka kan addinin musulunci da musulmi a kasar ta Amerika.
Kamfanin dillancin labarai na Ikna da ke kula da harkokin da suka shafi kur'ani mai girma a nan jamhuriyar musulunci ta Iran ne ya watsa rahoton cewa: duk da cewa kimanin kaso daya cikin dari na al'ummar Amerika musulmi ne amma duk da haka kaso sha uku cikin dari na musulmin Amerika ke fuskantar muzgunawa da takurawa misali a shekarar da ta gaba ta kawai an samu karuwar masu takuwa musulmi da masu tsananin nuna adawa da karan zuka kan addinin musulunci da musulmi a kasar ta Amerika.An nakalto daga majiyar mujallar Amerika ta Nation cewa;Mustapha Biyumi malamin jami'a a jami'ar Buruklin a birnin New York na kasar Amerika a cikin wata makala day a rubuta ya yi bayani dalla-dalla kan wannan mummunar dabi'a da kuma yadda ake takurawa musulmi a kasar Amerika a maimakon a zauna das u kamar kowa da ganinsu a matsin wani bangare na al'ummar Amerika da rayuwa tare das u ba tare da wata tsangwama ba amma kash bah aka lamarin yak e ba musamman a yan shekarun baya bayan nan da suke fuskantar takurawa da tsangwama.
1044072