IQNA

Kasashe Masu Girman kai ne Kan Gaba Wajen Take Hakkokin Dan Adam A duniya

17:20 - July 05, 2012
Lambar Labari: 2361552
Bangaren siyasa, kasashe masu girman kai na duniya su ne kan gaba wajen take hakkokin ‘yan adam duk kuwa da hargowar da suke yi wajen sukar wasu kasashe bisa dalilai na siyasa da cewa suna take hakkokin bil adama wanda hakan na bukatar fadakar sauran al’ummomin duniya baki daya.

Kamfanin dilalncin labaran iqna ya habarta cewa, ya nakalto daga shafin sadarwa na yanar gizo cewa, wasu yan majalisar dokokin Iran sun bayyana cewa kasashe masu girman kai na duniya su ne kan gaba wajen take hakkokin ‘yan adam duk kuwa da hargowar da suke yi wajen sukar wasu kasashe bisa dalilai na siyasa da cewa suna take hakkokin bil adama wanda hakan na bukatar fadakar sauran al’ummomin duniya baki daya kamar dai yadda salon siyasarsu ke gudana.
Jami'an Iran dai sun sha bayyana aniyarsu ta aiki tare da manyan kasashen duniyan wajen kawo karshen duk wani rashin fahimta da ya kunno kai a bangaren shirin nukiliyanta na zaman lafiya inda tsawon wadannan shekaru na tattaunawa ta tsaya kan wasu batutuwa guda uku a matsayin siyasarta a wannan fagen da suka hada da tsayin daka wajen tabbatar da hakkinta, amfani da hankali da girmama juna da kuma aiki a kas.
Dubi cikin tattaunawar baya-bayan nan tsakanin Iran da kasashen kungiyar 5+1 tun daga tattaunawar Istanbul na kasar Turkiya zuwa birnin Mosko na kasar Rasha ana iya bakar aniyar da manyan kasashen duniyar suke da ita kan Iran. A matsayin misali a tattaunawar farko ta birnin Istanbul, manyan kasashen duniya sun ki su amince da hakkin da Iran take da shi na amfani da makamashin nukiliya ta hanyar zaman lafiya da Iran take da shi. To amma sakamakon tsayin dakan Iran daga karshe dai a tattaunawar Istanbul ta biyu Madam Ashton din ta bayyana cewar manyan kasashen duniya za su girmama hakkin da Iran take da shi na mallakan fasahar nukiliya karkashin yarjejeniyar hana yaduwar makaman kare dangi NPT, haka nan kuma da aiki tare bugu da kari kan yin watsi da batun aiwatar da kudurin kwamitin tsaron MDD kan Iran a matsayin sharadin sake tattaunawa da Iran.
To sai dai kuma a tattaunawar da bangarorin biyu suka yi a birnin Bagadaza na kasar Iran, kasashen yammacin sun gabatar da wasu shawarwari da suke fatan Iran za ta amince da su inda ita ma Iran ta sake gabatar musu da wasu shawarwari guda biyar da take ganin idan aka bi su za a magance wannan matsalar. Su dai wadanann shawarwari na kasashen yammacin sun hada da cewa wajibi ne Iran ta dakatar da tace sinadarin uranium kashi 20 cikin dari da take yi sannan kuma ta rufe cibiyar nukiliyanta na Fordo da kuma mika uranium din da ta tace kashi 20 cikin darin zuwa ga kasashen yammaci, wanda dukkanin wadannan shawarwari suna nuni bakar aniyar da suke da ita da kuma yin karen tsaye ga maganar da suka yi a tattaunawar Istanbul din na cewa za su girmama hakkin da Iran take da shi na mallakan fasahar nukiliya na zaman lafiya.
Irin wadannan kwan gaba kwan baya da kasashen yammacin suke yi a yayin tattaunawar lamari ne da ke nuni da rashin kyakkyawar niyyar da suke da ita a kan Iran lamarin da ke sanya shakku cikin zukatan al'ummar Iran dangane da manufar kasashen yammaci. A saboda haka ne da dama suke ganin wannan tattaunawar da ake yi din za ta yi nasara ne kawai a lokacin da turawan suka bayyanar da kyakkyawar aniyarsu a fili sannan kuma suka yi watsi da duk wani nau'i na barazana da nuna girman kai. A lokuta da dama dai jami'an Iran sun ce tattaunawar za ta yi nasara ne kawai a lokacin da mayan kasashen duniyar suka yarda da hakkin da Iran take da shi na mallakan wannan fasaha sannan kuma suka nesanci yi mata barazana. Wannan kuma shi ne abin da Dakta Jalilin ya sake jaddawa cikin wasikar da ya aike wa Madam Ashton din.
1044786

captcha