IQNA

Makomar Kasar Libya Na Tattare Duhu Bayan da Kasashen Turai Suka Shige Mata Gaba

17:20 - July 05, 2012
Lambar Labari: 2361554
Bangaren kasa da kasa, Za a gudanar da zabe na farko a kasar Libya a ranar Asabar domin zabar majalisar kasa da zata maye gurbin hukumar wucin gadi wacce aka kafa a loikacin da jamaar kasar suka fara boren da ya kawar da marigayi Muammar Gaddafi, tun da farko dai an ajiye ranar 19 ga watan Yuni don gudanar da zaben amma aka dage shi saboda matsalolin tsare-tsare. Kimanin yan kasar Libya.

Kamfanin dillancin labaran iqna ya habarta cewa ya nakalto daga shafin sadarwa na yanar gizo na jaridar yaum sabi cewa, majalisar kasar da za a zaba a jibi Asabar da zata yi aiki a matsayin majalisar dokoki ta wucin gadi, tana da kujeru 200, 120 daga cikinsu yan indipenda ne ragowar 80 kuma za a zabe su a karkashin jamiyun siyasa.
Idan an zabi majalisar kasar zata nada kwamitin mutane 60 wadanda zasu rubuta sabon kundin tsarin mulki, Tsohon piraministan kasar Libya Bagdadi al-Mahmudi wanda aka maida shi gida daga kasar Tunisiya don ya fuskanci shari'a ya bayyana cewa bai aikata laifi ba kuma zai kare kansa a gaban kotu.
Al-Mahmudi ya sheda hakan ne wa manema labarai a yau a birnin Tiripoli cewa jamian maaikatar shari'a suna yi masa tambayoyi kusan a kowace rana, ya kuma kara da cewa a shirye yake mutanen kasar Libya su gurfanar da shi a gaban kuliya.
Hakazalika tsohon piraminstan na hambararriyar gwamanatin Gaddafi ya karyata zargin da ake yi na cewa an azabtar da shi a cikin kasarsa bayan da gwamnati kasar Tunisiya ta mika shi ga hukumommin Libya, yana mai cewa wannan magana da aka yayata tana nuni da wata manufa ta siyasa.
Da yan jarida suka matsa wa al-Mahmudi ta tambaya kan cewa mene ya sa ya ci gaba da goyon bayan Gaddafi har sai da gwamnatinsa ta fadi sai ya ce a gaban kotu ne zai kare kansa.
1044207





captcha