Kamfanin dilalncin labaran iqna ya habarta cewa dubban musulmin kasar Mali sun yi kakkausar da yin Allawadai da rusa wurare masu alfarma da suke kasar da mabiya tafarkin salafiya da ake kira ansaruddini suka yi a garin Tinbuktu da ke arewacin kasar da hakan ya hada da kabnrukan waliyayya da kuma dadaddun dakunan karatu na addinin muslunci wanda kuma wannan kungiya ta wahabiya tan ada dangantaka da kungiyar alkaida.
Kungiyar MNLA ta yan tawaye abzinawa yan aware a kasar Mali, ba sa rike da wani matsayi ko wani wuri mai mahimmanci a arewacin kasar mali. yankin da suka kwace yau da kusan watannin uku, an koresu daga garin Tombouctou, an murkushesu a Gao, yan tawayen na ji na gani kungiyoyin dake da'adawar musulumci Ansar Dine da Mujao, dake da alaka da Aqmi sun kwace ikon arewacin kasar ta Mali.
Ayar tambaya a nan ita ce: kenan mai kaza ya ci kai, da farko dai suke sahun gaba wajen fada da sojan kasar Mali da kwace yankin arewacin kasar, amma, kawayensu na jiya da suka kulla yarjejeniya da su Ansar Dine da Mujao, da ake kallo kamar wanda suka balle daga kungiyar Aqmi, reshen Al-Qaida a yankin Magreb, tun farkon tawayen a watan janeru yau sun koresu, sun dauri niyyar su reaba gari da abokan tafiyar ta su da suke kallo suna sakaki da addini.
Daga garin Gao da Kidal dake arewa maso gabacin kasar Mali, da yanzu yake karkashin ikon kungiyoyin masu ra'ayin islama, zuwa Tombouctou arewa maso yammacin kasar, a iya cewa an kaddamar da farautar yan tawayen, wasu na ganin bayan yantar da yankin na Azawad, yau an sace.
Yau an wayi gari sai an yi bincike kwakwaf kafin a gano takun sawun wani mayakin kungiyar tawayen yan aware a yankin a cewar wani dan jaridar kasar Mali day a lakanci batun tawayen arewacin kasar ta Mali mai suna Tiegum Bubeye Maiga. Kungiyar ta samu karbuwa a idon turawa da wasu kasashe makwabtan Mali saboda kasancewarta wadda bata yi batun addini ba, wanda hakan ya sa suka shagaltu da yin babatu a kafafen yada labaran kasar faransa maimakon irin ayukan da ya dace su yi a yankin na Azawad da suka kama kuma suka ainayancinsa.
A nasu waje kungiyoyin masu da'awar musulumci sun shirya tun farko yanda za su iya karbe milki ta hanyar raurana yan tawayen sannu a hankali. Masana irin wannan batu dake yin sharhi, sun nuna cewa sun ma yan tawayen dubara da hanasu amfani da manyan makaman da suka kawo daga kasar Libiya wanda ke boye a cikin duwatsu kasar ta Mali, sannan suka nuna dubaru da kwarewa da kuma karfin sojan da suke da a kan yan tawaye.
Abu na biyu na dubara mai mahimmanaci da suka yi shine: Sun jayo hankalin jama'a da sauran kabilu dake arewacin kasar ta Mali a yankunan da bugajen ba su da yawa ta hanyar raba musu abinci, da kalaman hadin kan kasa da hadewar kasar ta mali, sannan bayan da suka kwace garin Gao suka kore mayakan yan tawayen MNLA daga ofishin gwamna inda shadakwatarsu take sun daga tutar kasar Mali, hakan ya ma mutanen garin dadi ainun, sannan don kara samun karbuwa kungiyoyin sun bada rashawa kamar yanda wani ma'aikacin Diplomasiya ya shaida sun saye wani fitaccen shugaban kungiyar yan ainahin Gao, wanda ya juyya baya ga yan tawayen ya rungumi wadannan kungiyoyi.
Mayar da yan tawayen gefe guda zai iya kawo sauyi kan tattamnawa da ake yi kan yanda za a warware matsalar arewacin kasar. Ko dai yaya ta ke ciki yan tawayen sun dauki darasi na cewar ba za a taba cimma wata yarjejeniya mai dorewa da Mujahidai ba, kuma sun samar da Baraka mai girma tsakanin kungiyar yan tawayen. A yanzu dai yan tawayen na wasu kananan garuruwa kamar Gossi, Maneka Adarambukane, wata kila daga na n suna iya sake hadewa domin sake kwato garin na Gao, duk da yake wasu na ganin da wuya su iya samun nasara.
1045887