IQNA

Kungiyar Hamas Ta Bukaci A Kafa Kwamitin Bincike Kan Mutuwar Arafat

23:25 - July 08, 2012
Lambar Labari: 2363729
Bangaren kasa da kasa, kungiyar Hamas ta bukaci a kafa wani domin gudanar da bincike kan mutuwar Yasir Arfat wanda ake zargin cewa an sayar da shi guba wanda hakan ya zama sanadiyar ajalinsa duk kuwa da cewa kasashen turai da wasu daga kasashen larabawa suna ci gaba da nuna rashin amincewa da duk wani bincike da za a gudanar kan hakan.

Kamfanin dilalncin labaran iqna ya habarta cewa ya nakalto daga shafin sadarwa na yanar gizo cewa, kungiyar Hamas ta bukaci a kafa wani domin gudanar da bincike kan mutuwar Yasir Arfat wanda ake zargin cewa an sayar da shi guba wanda hakan ya zama sanadiyar ajalinsa duk kuwa da cewa kasashen turai da wasu daga kasashen larabawa suna ci gaba da nuna rashin amincewa da duk wani bincike da za a gudanar kan hakan musamman ma wasu daga cikinsu dama suna cikin wadanda ake zargi.
Marubucin kasar Masar Ala Aswani ya ce mika mulkin kasar Masar ga hannun Ahmad shafiq tsohon pita ministan kasar lokacin mulkin tsohon shugaban mulkin kama karya Husni Mubarak hakan na nufin cewa juyin juya halin da al’ummar kasar suka yi ya kawo karseh kenan domin wadanda aka kawar sun dawo.
mambobin majasar dokokin kasar Masar sun yi kira da a safke babban malamin kasar mai bayar da fatawa bayan ya yi tafiya zuwa haramtacciyar kasar Isra’ila ba tare da izinin majalisa da kuma yin shawara da majalisar malaman addinin muslunci ta kasar ba lamarin da ake kallonsa a matsayin wani babban kure.
Tafiyar da Ali Juma’a ya yi zuwa birnin Qods ya yi ne tare da hadin gwiwa da ma’aikatar tsaro ta haramatcciyar kasar Isra’ila wanda kuma ko shakka babu hakan ya sanya gagarumin shakku a cikin zukatan mutanen kasar dangane da wannan ziyara tasa, duk kuwa da cewa daga cikin abubuwan da ya yi har da duba lafiyarsa a asibiti. 1045948
captcha