IQNA

Mabiya Tafarkin Iyalan Gidan Manzo Sun Gudanar da Taron Nisf Sha’aban

23:29 - July 08, 2012
Lambar Labari: 2363730
Bangaren kasa da kasa, duk da irin matakan rashin imani da mahukuntan kasar Saudiyya suke dauka kan mabiya tafarkin iyalan gidan manzon Allah da suke kasar sun gudanar da zaman taro na raya daren goma sha biyar ga watan Sha’aban wanda ya yi daidai da ranar haihuwar limami na goma sha biyu daga cikin limaman shiriya na ahlul bait amincin Allah ya tabbata a gare su.
Kamfanin dillancin labaran iqna ya habarta cewa ya nakalto daga shafin sadarwa na yanar gizo cewa duk da irin matakan rashin imani da mahukuntan kasar Saudiyya suke dauka kan mabiya tafarkin iyalan gidan manzon Allah da suke kasar sun gudanar da zaman taro na raya daren goma sha biyar ga watan Sha’aban wanda ya yi daidai da ranar haihuwar limami na goma sha biyu daga cikin limaman shiriya na ahlul bait amincin Allah ya tabbata a gare su da kuma yadda suke samun ci gaba daga bangarori daban-daban.
A nasa bangaren jagoran juyin juya halin musulunci a Iran Ayatullah Ali Khamenei, yayi wannan furuci ne jiya litinin yayin da ya gana da praministan kasar ta Iraki Nuri Almaliki, da ya kawo wata ziyara a nan Teheran. Jagoran ya kara da cewa, kokarin da zai taimaka wajen kara tabbatar da karfin magabatan kasar ta Iraki, musamman game da jihadi na kimiya hade da ayukan sake gina kasar, sune za su habbaka matsayin kasar da cimma guri da bukatun al'ummar kasar da ma gwamnatin kasar baki daya. Inda ya nuna cewar irin abubuwan da suka gudana a cikin kasar a yan watannin nan, sun farkar da gwamnati da al'ummar kasar game da irin matsayi da kuma rawar da za su iya takawa a cikin duniyar larabawa da musulmi.
A mahangar jagoran juyyin juyya halin musulumci, fucewar daukacin sojojin kasar Amurka daga kasar Iraki na daga cikin manyan abubuwa masu mahimmanci da suka ja hankali kuma wanda aka yi galaba kansu, da suka biyo bayan namijin kokari da kishin kasar da jama'ar kasar Iraki suka nuna, Sannan, karbar bakoncin taron kungiyar hadin kan larabawa da kasar ta Iraki ta yi ya kara nuna karfin gwamnatin kasar. Ayatullah Ali Khamenei, ya kara da cewa, Wasu bangarori sun yi ta kokarin nuna cewa kasar Iraki, ba ta da wani matsayi a cikin kasashen larabawa, amma bayan taron kungiyar hadin kan kasashen larabawa da ta gudana a Bagdada, kasar Iraki, a yanzu na kan gaba a cikin wannan kungiyar, kuma praministan kasar ke jagorantar ta. 1045958






captcha