Bnagren siyasa da zamantakewa: an yi wata ganawa da tattauanwa tsakanin babban sakataren kungiyar hadin kan musulmin duniya da kuma babban mai bada fatawa a kasar uzbakistan kuma shugaban da ke kula da ofishin da ke kula da lamura da suka shafi musulmi a wannan kasar kuma an yi wannan ganawa ce a birnin Makka na kasar Saudiya.
Kamfanin dillancin labarai na Ikna da ke kula da harkokin da suka shafi Kur'ani mai tsarki a nan jamhuriyar musulunci ta Iran ne ya watsa rahoton cewa; an yi wata ganawa da tattauanwa tsakanin babban sakataren kungiyar hadin kan musulmin duniya da kuma babban mai bada fatawa a kasar uzbakistan kuma shugaban da ke kula da ofishin da ke kula da lamura da suka shafi musulmi a wannan kasar kuma an yi wannan ganawa ce a birnin Makka na kasar Saudiya.Abdallah bin AbdulMuhsin Alturki babban sakataren kungiyar hadin kan musulmi duniya da kuma Usman Khan Ali Uf babban mai bayar da fatawa a kasar Uzbakistan sun tattauna lamuran da suka shafi musulmi da harkokin musulmin da sauran lamuran musulmi a duniya da kuma irin matsaloli barkatai da musulmi ke fuskanta da kuma yadda za a kara habaka hadin kai a tsakanin musulmi a fadin duniya.
1046585