IQNA

An Fara Gudanar Da Taron Fadakar Musulmi Na Mata A Borj Milad

23:45 - July 11, 2012
Lambar Labari: 2366621
Bangaren kasa da kasa, an fara gudanar da taron fadakar musulmi na kasashen duniya tare da halartar masana daga sassa na duniya da adadinsu yah aura dubu daya da dari biyu kamar dai yadda bangarorin da suke daukar nauyin taron suka bayyana ga manema labarai yau a birnin Tehran.
Kamfanin dillancin labaran iqna ya habarta cewa, ya nakalto daga shafin sadarwa na yanar gizo cewa, an fara gudanar da taron fadakar musulmi na kasashen duniya tare da halartar masana daga sassa na duniya da adadinsu yah aura dubu daya da dari biyu kamar dai yadda bangarorin da suke daukar nauyin taron suka bayyana ga manema labarai yau a fadar mulkin jamhuriyar muslunci.
Dubi cikin tattaunawar baya-bayan nan tsakanin Iran da kasashen kungiyar 5+1 tun daga tattaunawar Istanbul na kasar Turkiya zuwa birnin Mosko na kasar Rasha ana iya bakar aniyar da manyan kasashen duniyar suke da ita kan Iran. A matsayin misali a tattaunawar farko ta birnin Istanbul, manyan kasashen duniya sun ki su amince da hakkin da Iran take da shi na amfani da makamashin nukiliya ta hanyar zaman lafiya da Iran take da shi. To amma sakamakon tsayin dakan Iran daga karshe dai a tattaunawar Istanbul ta biyu Madam Ashton din ta bayyana cewar manyan kasashen duniya za su girmama hakkin da Iran take da shi na mallakan fasahar nukiliya karkashin yarjejeniyar hana yaduwar makaman kare dangi haka nan kuma da aiki tare bugu da kari kan yin watsi da batun aiwatar da kudurin kwamitin tsaron kan Iran a matsayin sharadin sake tattaunawa da Iran.
To sai dai kuma a tattaunawar da bangarorin biyu suka yi a birnin Bagadaza na kasar Iran, kasashen yammacin sun gabatar da wasu shawarwari da suke fatan Iran za ta amince da su inda ita ma Iran ta sake gabatar musu da wasu shawarwari guda biyar da take ganin idan aka bi su za a magance wannan matsalar. Su dai wadanann shawarwari na kasashen yammacin sun hada da cewa wajibi ne Iran ta dakatar da tace sinadarin uranium kashi 20 cikin dari da take yi sannan kuma ta rufe cibiyar nukiliyanta na Fordo da kuma mika uranium din da ta tace kashi 20 cikin darin zuwa ga kasashen yammaci, wanda dukkanin wadannan shawarwari suna nuni bakar aniyar da suke da ita da kuma yin karen tsaye ga maganar da suka yi a tattaunawar Istanbul din na cewa za su girmama hakkin da Iran take da shi na mallakan fasahar nukiliya na zaman lafiya.
1049302


captcha