Kamfanin dillancin labaran iqna ya habarta cewa, ya nakalto daga shafi9n sadarwa na yanar gizo cewa, Ramin mehman parast kakakin ma’aikatar harkokin wajen jamhuriyar muslunci ta Iran ya mayar da kakkausan martani kan cin zarafin mabiya tafarkin iyalan gidan manzon Allah da mahukuntan kasar Saudiyya suke musamman tun bayan kama babban malamain yankin Katif sheikh Namir cikin makonnan da muke ciki a wani sabon mataki na kare manufofin yahudawan sahyuniya a yankin.
A wani rahoto da jami'ar Tel Aviv ta HKI ta fitar an bayyana cewar kasar Saudiyya ita ce fata sannan kuma garkuwa ta karshe wajen karewa da kuma tabbatar da manufofin HKI a kasashen larabawa sakamakon gazawar da sauran kasashen larabawan suka yi wajen tabbatar da hakan.
Rahoton ya kara da cewa sakamakon irin adawar da kasar Saudiyya take nuna wa Jamhuriyar Musulunci ta Iran don haka ita ce garkuwa ta karshe ga HKI daga abin da suka kira barazanar Iran. Rahoton ya kara da cewa 'ya'yan gidan sarautar Al-Sa'ud dake mulkin Saudiyyan suna da muhimmanci ga HKI sakamakon himmar da suka bayar wajen fada da tasirin Iran a kasashen Yemen, Masar, Iraki da kuma Labanon.
A kwanakin baya ma dai wasu bayanan sirri dangane da alakar Saudiyya da kungiyar leken asirin HKI da shafin nan na Wikileaks ya fitar na nuni da cewa Saudiyya na aiki da kungiyar MOSSAD din wajen tattaro bayanai kan Iran da yadda za a yi da ita.
An jima dai ana sukan Saudiyyar saboda alaka ta boye da take da ita da HKI wajen rarraba kan al'ummar musulmi da raunana su kamar yadda a halin yanzu yake faruwa a kasar Siriya da sauransu.
1050622