Bangaren fikira, an samu halartar masana daga sassa na duniya a babban taron fadakar musulmi wanda ya kasance shi ne irinsa na farjko da ya kebanci mata musulmi masana da suka gabatar da jawabai da makaloli da suka haura dari biyar kamar dai yadda masu kula shirya zaman taron suka bayyana.
Kamfanin dilalncin labaran iqna ya habarta cewa ya nakalto daga shafin sadarwa na yanar gizo cewa, an samu halartar masana daga sassa na duniya a babban taron fadakar musulmi wanda ya kasance shi ne irinsa na farjko da ya kebanci mata musulmi masana da suka gabatar da jawabai da makaloli da suka haura dari biyar kamar dai yadda masu kula shirya zaman taron suka bayyana ga manema labarai bayan kammala zaman taron.
A bangare guda kuma a yau bakin da suke halartar taron duniya kan fadakar al’ummar musulmi sun gana da jagoran juyin juya halin muslunci inda ya gabatar musu da jawabai dangane da matsayin wannan fadaka da ake shidawa a halin yanzu a cikin kasashen musulmi da na larabawa da kuma muhimmancin zama cikin fadaka dangane da yadda makiya muslunci suke kokarin ganin sun sace yunkurin musulmi domin kare manufofinsu na siyasa tare da kawar da hakinin manufar juyin al’umma.
Jagoran juyin juya halin Musulunci Ayatullah Sayyid Ali Khamenei ya bayyana cewar kasashen yammaci ba su fahimci cewa ta hanyar sanya wa Iran takunkumi suna kara wa al'ummar kasar karfin gwuiwa ne wajen fada da duk wata barazana a kansu kamar yadda suka yi shekaru talatin da wani abin da suka wuce ba.
Jagoran ya bayyana hakan ne a lokacin ganawarsa da mahalarta taro na farko na kasa da kasa kan mata da farkawa ta Musulunci da ke faruwa da aka gudanar a Tehran inda ya ce tsaron shekaru talatin din da suka gabata al'ummar Iran sun tsaya kyam wajen fuskantar duk wani takuri daga makiya ta hanyar sadaukar rayuwarsu da dukiyoyin da ababen kaunarsu, wanda hakan ne ya sanya a halin yanzu Iran ta zamanto mai karfi sama da yadda take a da a lokutan baya.
1050133