Bangaren kasa da kasa, ma’aikatar kula da harkokin addini a kasar Tunisia na yin iyakacin kokarinta domin ganin ta fatatattki yan salafiyya masu rike da wasu daga cikin msallatan kasar inda suke kafirta sauran musulmi tare da yin kira na tashin hankali da raba kan al’ummar musulmi baki daya.
Kamfanin dillancin labaran iqna ya habarta cewa ya nakalto daga shafin sadarwa na yanar gizo na kapitalis cewa, ma’aikatar kula da harkokin addini a kasar Tunisia na yin iyakacin kokarinta domin ganin ta fatatattki yan salafiyya masu rike da wasu daga cikin msallatan kasar inda suke kafirta sauran musulmi tare da yin kira na tashin hankali da raba kan al’ummar musulmi baki daya musamman a yankunan da suke ganin suna da bakin fada aji.
A wani labarin kuma uku daga cikin ma'aikatan diplomasiyyar kasar Aljeriya 7 da aka sace a garin Gao na Arewacin kasar Mali sun kai ga samun 'yancinsu a yau alhamis kamar dai yadda kakakin kungiyar Mujao wato daya daga cikin kungiyoyin 'Yan sallafiya da suka sace su ya bayyana wa manema labarai.
Adnan Abu Walid Shahraoui wanda ya bayyana kansa a matsayin mai magana da yawun kungiyar ta 'yan Alqa'ida shi ne ya tabbatar da hakan duk da cewa bai bayyana dalilan kungiyar na sakin wadannan mutane uku ba, sannan kuma ya ki ya yi karin bayani a game da makomar sauran ma'aikatan diplomasiyyar na Aljeriya su 4 da suka rage a hannun kungiyarsu ba.
Tun a ranar 5 ga watan Afrilun da ya gabata ne dai, wato a kutsen farko da mayakan suka yi a birnin Gao da ke Arewacin Mali suka cafke 'yan kasar ta Aljeriya.
1050132