Bangaren kasa da kasa, an gudanar da janazar mutane biyu da suka yi shahada a yankin Katif na gabacin kasar Saudiyya da jami’an tsaron kasar suka kashe har lahira tare da umurnin mahukunta domin sun nuna rashin gamsuwarsu da matakin kama sheikh Namir wanda yake kira zuwa yin gyara da samar da sauyi na adalci a harkokin mulkin kasar.
Kmafanin dillancin labaran iqna ya habarta cewa, yanakalto daga shafin sadarwa na tashar talabijin din rasid cewa an gudanar da janazar mutane biyu da suka yi shahada a yankin Katif na gabacin kasar Saudiyya da jami’an tsaron kasar suka kashe har lahira tare da umurnin mahukunta domin sun nuna rashin gamsuwarsu da matakin kama sheikh Namir wanda yake kira zuwa yin gyara da samar da sauyi na adalci a harkokin mulkin kasar wadda yahudawan sahyuniya tare da turawa suke iko da ita, ta hanyar karnukan farautarsu da suke kan sarauta.
Kakakin ma’aikatar harkokin wajen jamhuriyar muslunci ta Iran ya mayar da kakkausan martani kan cin zarafin mabiya tafarkin iyalan gidan manzon Allah da mahukuntan kasar Saudiyya suke musamman tun bayan kama babban malamain yankin Katif sheikh Namir cikin makonnan da muke ciki a wani sabon mataki na kare manufofin yahudawan sahyuniya a yankin.
A wani rahoto da jami'ar Tel Aviv ta HKI ta fitar an bayyana cewar kasar Saudiyya ita ce fata sannan kuma garkuwa ta karshe wajen karewa da kuma tabbatar da manufofin HKI a kasashen larabawa sakamakon gazawar da sauran kasashen larabawan suka yi wajen tabbatar da hakan.
Rahoton ya kara da cewa sakamakon irin adawar da kasar Saudiyya take nuna wa Jamhuriyar Musulunci ta Iran don haka ita ce garkuwa ta karshe ga HKI daga abin da suka kira barazanar Iran. Rahoton ya kara da cewa 'ya'yan gidan sarautar Al-Sa'ud dake mulkin Saudiyyan suna da muhimmanci ga HKI sakamakon himmar da suka bayar wajen fada da tasirin Iran a kasashen Yemen, Masar, Iraki da kuma Labanon.
1050230