IQNA

An Bude Baje Kolin Tufafin Muslunci A kasar Thailand Domin Tarbar Watan Ramadan

Bangaren al’adu da fasaha, an bude baje koli na tufafin muslunci a kasar Thailand domin fara shirin tarbar watan Ramadan mai alfarma wanda yanzu haka kamfanoni na ci gaba da kai nasu kayayyakin zuwa wurin da ake gudanar da wannann babban baje koli a birnin Bankuk fadar mulkin kasar.
Kamfanin dilalncin labaran iqna ya habarta cewa ya nakalto daga shafin sadarwa na yanar gizo cewa, an bude baje koli na tufafin muslunci a kasar Thailand domin fara shirin tarbar watan Ramadan mai alfarma wanda yanzu haka kamfanoni na ci gaba da kai nasu kayayyakin zuwa wurin da ake gudanar da wannann babban baje koli a birnin Bankuk fadar mulkin kasar ta Thailand wadda tana daya daga cikin kasashe da ke da musulmi a yanin Asia.
A wani labarin kuma kotun koli na kasar Pakistan ta yi barazanar tube Priministan kasar mai ci idan shima ya kasa bin umurninta na yin binciken da ya dace kan almundahanar kodaden jama'a wanda ake zargin shugaban kasar ta Pakistan Asif Ali Zardari da yi.
Kamfanin dillancin labaran kasar Farabsa AFP ya bayyana cewa, alkalin kotun Asif Sa'eed Khosa ya aike da wasika ga Priministan kasar Raja Parviz Ashraf a yau Alhamis inda ya bukace shi da ya fara bincike tare da bankin Swizland kan kudaden da ake zargin shugaba Zardari ya ajiye a can, kuma ya bashi nan da ranar 25 ga wannan watan da muke ciki ya aiko masa da sakamakon binciken da ya yi, ko kuma ya fuskanci kora daga kojerarsa kamar yadda ya kori Yusuf Riza Gilani a cikin watan da ya gabata.
Kotun kolin kasar Pakistan dai ta yi watsi da dokar yin afawa ga yan siyasar kasar Pakistan kimani 8000 wanda shugaban kasar Pakistan na lokacin Parviz Musharraf ya yi a cikin watan december shekara ta 2009 kan zargin almundahanan da suka yi da kudaden jama'a. Shugaban kasar Asif Ali Zardari dai yana daga cikin wadanda Musharraf din ya yiwa afwar.
1049002