IQNA

Imam Khomini (RA) Ya Bayyana Tsarin Addini Da Siyasa A Aikace

17:45 - July 13, 2012
Lambar Labari: 2367319
Bangaren siyasa da zamankewa, malaman addini da masana a kasar Pakistan sun bayyana cewa marigayi Imam Khomeini (RA) wanda ya kafa jamhuriyar muslunci ta Iran shi ne wanda ya aikata addini tare da siyasa a cikin wannan zamani damuke rayuwa ta hanyar kafa gwamnatin muslunci da take tafiya daidai da koyarwar muslunci.
Kamfanin dilalncin labaran iqna ya habarta cewa, ya nakalyo daga shafin sadarwa na yanar gizo na bangaren gabacin nahiyar Asia, malaman addini da masana a kasar Pakistan sun bayyana cewa marigayi Imam Khomeini (RA) wanda ya kafa jamhuriyar muslunci ta Iran shi ne wanda ya aikata addini tare da siyasa a cikin wannan zamani damuke rayuwa ta hanyar kafa gwamnatin muslunci da take tafiya daidai da koyarwar muslunci kuma har y7anzu ba ta nuna gazawa ba duk da matsin lamba.
Jagoran juyin juya halin Musulunci Ayatullah Sayyid Ali Khamenei ya bayyana cewar kasashen yammaci ba su fahimci cewa ta hanyar sanya wa Iran takunkumi suna kara wa al'ummar kasar karfin gwuiwa ne wajen fada da duk wata barazana a kansu kamar yadda suka yi shekaru talatin da wani abin da suka wuce ba.
Jagoran ya bayyana hakan ne a lokacin ganawarsa da mahalarta taro na farko na kasa da kasa kan mata da farkawa ta Musulunci da ke faruwa da aka gudanar a Tehran inda ya ce tsaron shekaru talatin din da suka gabata al'ummar Iran sun tsaya kyam wajen fuskantar duk wani takuri daga makiya ta hanyar sadaukar rayuwarsu da dukiyoyin da ababen kaunarsu, wanda hakan ne ya sanya a halin yanzu Iran ta zamanto mai karfi sama da yadda take a da.
Yayin da ya koma kan rawar da mata suke takawa wajen ciyar da al'umma gaba da kuma farkar da al'umma, Jagoran ya ce rawar da suke takawa din rawa ce mai muhimmanci yana mai cewa duk wani yunkurin neman sauyi da mata suka shigo cikinsa to kuwa zai yi nasara.
A jiya ne dai aka kawo karshen wannan taron wanda ya sami halartar mata 1,500 daga kimanin kasashe 80 na duniya.
1050488

captcha