IQNA

Masu Kishin Islama A Jordan Za Su Kaurace Wa Zaben Da Za a Gudanar A kasar

17:45 - July 13, 2012
Lambar Labari: 2367322
Bangaren kasa da kasa, kungiyar ikhwan a kasar Jordan ta sanar cewa za ta kauracewa zaben ‘yan majalisar dokoki da za a gudanar daga nan zuwa karshen wannan shekara akasar domin alamu sun fara nunawa tun ayanzu cewa masarautar kasar na shirin tafka magudi domin bayar da nasara ga masu goyon bayanta.
Kmafanin dilalncin labaran iqna ya habarta cewa ya nakalto ndaga shafin sadarwa na yanar gizo na jaridar Al-ayyam ta palastinu cewa, kungiyar ikhwan a kasar Jordan ta sanar cewa za ta kauracewa zaben ‘yan majalisar dokoki da za a gudanar daga nan zuwa karshen wannan shekara akasar domin alamu sun fara nunawa tun ayanzu cewa masarautar kasar na shirin tafka magudi domin bayar da nasara ga masu goyon bayanta kamar dai yadda kakakin kungiyar ya fada.
Wani labarin kuma yana cewa Wata majiya ta gwamnatin Siriya ta bayyana cewar tun bayan fitar da labarin cewa jakadan kasar a Iraki Nawwaf Faris ya yi murabus daga mukaminsa da kuma komawa cikin masu adawa da gwamnatin kasar, jami'ai a Siriyan suke ta kokari wajen magana da shi amma lamarin ya ci tura inda suke cewa akwai yiyuwar an sace shi ne da tilasta masa fadin abin da ya fadin.
Majiyar ta kara da cewa hatta ma'aikatan ofishin jakadancin Siriyan a Iraki da kuma iyalan jakadan ba su da labarin inda ya ke lamarin da ke kara karfin zaton da ake yi na cewa mutanen da suke da alaka da 'yan adawan Siriyan ne suka sace shi.
A jiya ne dai tashohin Aljazeera na kasar Qatar da Al-Arabiyya ta Saudiyya wadanda suka yi kaurin suna wajen fada da gwamnatin Siriya da yada kararraki kan abin da ke faruwa a can din suna sanar da murabus din jakadan na Siriya da kuma komawa cikin 'yan adawan.
Majiyar ta Siriya taci gaba da cewa za su gaba da neman inda jakadan yake don tabbatar da gaskiya ya yi murabus din ne ko kuma sace shi aka yi.
1051669

captcha