IQNA

An Kira Da Saka Ranar Makoki Ta Tunawa Da kisan Musulmin Bosnia

18:00 - July 14, 2012
Lambar Labari: 2368176
Bangaren kasa da kasa, an yi kira da saka ranar makoki ta tunawa da kisan gilla da sabiyawa suka yi wa musulmin kasar Bosnia a shekarun baya domin kada duniya ta manta da cin zarafin da aka yi wa musulmi tare da taimakon manyan kasashen yammacin turai da suke raya kare hakkokin dan adam.
Kamfanin dilalncin labaran iqna ya habarta cewa ya nakalto daga shafin sadarwa na yanar gizo na OCI cewa an yi kira da saka ranar makoki ta tunawa da kisan gilla da sabiyawa suka yi wa musulmin kasar Bosnia a shekarun baya domin kada duniya ta manta da cin zarafin da aka yi wa musulmi tare da taimakon manyan kasashen yammacin turai da suke raya kare hakkokin dan adam a ka karya da munafunci.
A wata sanarwa da ta fitar a safiyar yau asabar, ma'aikatar harkokin wajen kasar Iran ta bayyana cewa akwai bukatar Kungiyoyi da kuma kasashen duniya su farga sannan kuma su gudanar da bincike domin gano tare da hukunta wadanda ke hannun wajen aikata kisan kiyashi a kan musulmin garin Sebrenica na kasar Bosnia.
Sanarwar wacce aka fitar a daidai lokacin da ake juyayin zagayowar ranar aiwatar da wannan kisan kiyashi, ta ce kisan musulmi akalla dubu 8 da al'ummar Sabiya suka yi a ranar 11 ga watan Yulin shekarar 1995, wani babban bala'i ne da kuma zalunci da aka aikata akan musulmi, saboda haka nauyi ya rataya a kan kasashen duniya domin kamawa tare da hukunta duk wadanda suke da hannu a wannan lamari.
Kasar ta dai Iran ta ce kin hukunta wadanda suka aikata wannan aiki na assha, wani abin damuwa ne ga al'ummar duniya, sannan kuma wata alama ce da ke kara tabbatar wa duniyar cewa kungiyoyin da ke ikirarin kare hakkokin bil'adama a wannan zamani akwai son-rai a cikin ayyukan da suke gudanarwa.
1051641





captcha