IQNA

Mahukuntan Saudiyya Sun Sake Kashe Wani Matashi A Yankin Gabacin Kasar

13:27 - July 15, 2012
Lambar Labari: 2368836
Bangaren kasa da kasa, mahukuntan kasar Saudiyya sun sake kashe wani matashi mai suna Abdullah Ajami a yankin Katif da ke gabacin kasar wanda ya kasance daya daga cikin masu nuna rashin amincewarsu da kame bababn malamin yankin da mahukuntan wahabiyawan Saudiyya suka yia acikin makon day a gabata.

Kamfanin dilalncin labaran iqna ya habarta cewa ya nakalto daga shafin sadarwa na yanar gizo na tashar talabijin din Alalam cewa, a jiya mahukuntan kasar Saudiyya sun sake kashe wani matashi mai suna Abdullah Ajami a yankin Katif da ke gabacin kasar wanda ya kasance daya daga cikin masu nuna rashin amincewarsu da kame bababn malamin yankin da mahukuntan wahabiyawan Saudiyya suka yia acikin makon day a gabata saboda ra'ayinsa na neman yanci day a shara da su.

Rahotanni sun ce da dama daga cikin limaman juma'a yankunan da daman a kasashen larabawa sun nuna goyon bayansu ga sheikh Namir da mahukuntan Saudiyya suka kames hi bisa zarginsa da tunzura jama'a su kyamaci mahukuntan mulkin kama karya da fir'ananci na kasar ta Saudiyya da ba ta san labarin wani abu wais hi demokradiyya ba amma kuma suna taimakon yan ta'adda a wasu kasashe da sunan neman kafa ta.

Dangane da batun kasar da ziyarar da sakatariyar harkokin wajen Amurka takai kasar kuwa, wasu daga cikin kasashen larabawa da suke dasawa da Amurka kuma suke kare manufofinta a cikin kasashen larabawa da na musulmi a halin yanzu kamar ita kanta Saudiyya da hadaddiyar daular larabawa, ba su lale marhabin da zabar Mursi a matsayin shugaban kasar Masar ba, domin kuwa sun yi iyakacin kokarinsu wajen kasha biliyoyin kudade domin muguda sakamakon zaben na kasar Masar da nufin kayar da Mursi amma hakan bai kai ga nasara ba, wannan ne ma ya sanya Mursi yake kokarin tabbatarwa irin wadannan kasashen larabawa da cewa ba zai mayar da hankali kan abubuwan da suka faru ba, maimakon haka yana neman hadin kansu domin tunkarar gaba.
Yanzu dai za a iya cewa kasashen Amurka da sauran kawayenta larabawa musamman Saudiyya, suna baiwa Mursi rata ne domin su ga kamun luddayinsa, idan har zai iya tafiya da salon siyasa da zai kare manufofinsu, ko da kuwa bai kai kamar yadda babban aminsu Husni Mubarak ya kasance yanayi ba, to za su iya daga masa kafa, a matsayin rashin uwa a kan yi uwa daki.
1052639





captcha