Bangaren kasa da kasa, an gudanar da gasar karatu da hardar kur’ani mai tsarki ta yankin Saihat da aka saba gudanarwa akowace shekara kamar dai yadda majiyoyin bangarorin da suke da shirya gasar suka sanar a cikin makon da ya kama wanda yanazu haka ake ci gaba da sauraren sakamakon karshe na wadanda suka lashe mataki na daya da na biyu da uku.
Kamfani9n dilalncin labaran iqna ya habarta cewa ya nakalto daga shafin sadarwa na yanar gizo na rasid cewa, an gudanar da gasar karatu da hardar kur’ani mai tsarki ta yankin Saihat da aka saba gudanarwa akowace shekara kamar dai yadda majiyoyin bangarorin da suke da shirya gasar suka sanar a cikin makon da ya kama wanda yanazu haka ake ci gaba da sauraren sakamakon karshe na wadanda suka lashe mataki na daya da na biyu da uku a wannan gasa da aka kammala.
A wani batun na daban kuma shugabannin kasashen Masar da Tunusiya sun jaddada wajabcin warware matsalar Palasdinu ta hanyar adalci, a taron manema labarai da suka gudanar a yau juma'a a birnin Alkahira na Masar; shugaban kasar Masar Muhammad Mursi da takwaransa na Tunusiya Muhammad Munsif Almarzuki sun bayyana goyon bayansu ga al'ummar Palasdinu tare da jaddada wajabcin daukan dukkanin matakan da suka dace wajen ganin an warware matsalar Palasdinu ta hanyar adalci.
Har ila yau shugabannin kasashen biyu sun bukaci kawo karshen sabanin da ke tsakanin Palasdinawa musamman manyan kungiyoyin Palasdinawa na Hamas da Fatah, duk da cewa an samu canji a cikin matsayin kungiyoyin biyu wadanda suka shafe tsawon lokaci suna gaba da juna, sakamakon cewa a lokacin daya bangaren na tare da yahudawa daya bangaren kuma tare da gwagwarmayar neman yanci.
1052625