IQNA

Wani Dan kasar Holland Ya Karbi Addinin Muslunci A Kasar Turkiya

17:42 - July 15, 2012
Lambar Labari: 2369086
Bangaren siyasa da zamantakewa, wani dan kasar Turkiya mai yawon bude ido a kasar Turkiya ya karbi addinin mulusnci inda ya furta Kalmar shahada tare da yadda da cewa addinin muslunci shi ne addinninsa na rayuwa kuma ya karbi kwafi na kur’ani mai tsarki da littafai da za su koyar da shi addininsa.
Kamfanin dilalncin labaran iqna ya habarta cewa ya nakalto daga shafin sadarwa na yanar gizo na bangaren yada labaransa a nahiyar Asia wani dan kasar Turkiya mai yawon bude ido a kasar Turkiya ya karbi addinin mulusnci inda ya furta Kalmar shahada tare da yadda da cewa addinin muslunci shi ne addinninsa na rayuwa kuma ya karbi kwafi na kur’ani mai tsarki da littafai da za su koyar da shi addininsa kamar dai yadda majoyin suka tabbatar.
A wani labarin na daban kuma jiya ne sakatariyar harkokin wajen kasar Amurka H. Clinton ta gana da shugaban kasar Masar Muhammad Mursi a ziyarar aiki da take gudanarwa a kasar ta Masar, wadda irinta ce ta farko da ta kai kasar tun bayan zaben Mursi a matsayin sabon shugaban kasar a cikin watan Yunin da ya gabata.
Jim kadan bayan ganawar da ta gudana tsakaninta da sabon shugaban kasar ta Masar, H. Clinton ta gudanar da taron amnema labarai tare da takwaranta na kasar Masar Muhammad Amru, inda ta bayyana cewa ganawarta da Muhammad Mursi ta yi armashi matuka, ta ce manufar ziyarar tata dai ita ce nuna cikakken goyon bayan Amurka ga tsarin demokradiyya a kasar Masar, wadda ta kasance sakamako ne na sadukantarwar da al'ummar kasar suka yi.
Wani babban jami'i a ma'aikatar harkokin wajen kasar Amurka ya fadi cewa daga cikin muhimamn abubuwan da Clinton take zantawa da jami'an kasar Masar kansu, akwai batun yarjejeniyar zaman lafiya da haramtacciyar kasar Isra'ila, wadda Masar ita ce kasa ta farko a cikin kasashen larabawa da fara rattaba hannu kan irin wannan yarjeneiya tare da gwamnatin yahudawan Sahyuniya a cikin shekara ta 1979, a lokacin mulkin Anwar Sadat, wanda hakan ya fuskanci kakkausar suka daga a'ummar Masar da ma sauran al'ummomin larabawa da na musulmi a duniya, kuma har inda yau take Masar na nan daram kan wannan yarjejeniya.
1052674

captcha