Kamfanin dillancin labaran iqna ya habarta cewa ya nakalto daga shafin sadarwa na yanar gizo na cibiyar kusanto da mazhabobin muslunci ta duniya cewa, babban sakataren cibiyar Ayatollah Mohsen Aaraki ya bayyana cewa marigayi Imam Khomeini (RA) ya yantar da tunanin musulmi daga danniyar kasashe masu girman kai tare da nuna musu hanyar zama cikin yanci na tunai da siyasa da kuma tabbatar da cewa wannan ya ci gaba har zuwa zamuna masu a nan gaba da hakan zai zama tamkar wata katangar karfe ga wannan salon siyasa ta zalunci.
Tun bayan jerin kisan gillan da aka yi wa wasu daga cikin masanan nukiliyan kasar Iran da kuma bayanan da jami'an tsaron kasar suka fitar da ke nuni da hannun HKI cikin hakan bayanai suke ci gaba da fitowa da suke tabbatar da wannan ikirari na Iran din. Bayani na baya-bayan nan shi ne wanda dan jaridar tashar talabijin din nan na Amurka CBS Dan Raviv da kuma Yossi Melman wanda shi ma dan jarida ne a HKI suka fitar cikin wani sabon littafi da suka buga mai sunan 'Spies Against Armageddon' inda a cikin littafin suka yi karin haske dangane da hannun da take da shi wajen kisan gillan da aka yi wa masanan na Iran cikin 'yan shekarun nan.
A wata tattaunawa da ya yi da tashar CBS din, Dan Raviv ya bayyana cewar a cikin kungiyar leken asirin akwai wani bangare da aka ware da aka ba su aikin kashe masanan nukiliyan Iran. Har ila yau a cikin wannan littafin, marubucin ya yi ishara da wasu daga cikin ayyukan ta'addanci da kisan gilla da kungiyar din ta aikata a biranen Beirut da Damaskus na kasashen Labanon da Siriya inda yake cewa a halin yanzu 'yan kungiyar leken asirin Amurka da HKI suna aiki tare wajen ganin sun dakatar da shirin nukiliyan. Daga cikin ayyukan da suke gudanarwa tare da har da aiko da 'virus' zuwa ga kwamfutocin cibiyoyin nukiliyan na Iran da kuma ci gaba da tattaro bayanai kan masanan na Iran.
Dangane da wannan batu na aiko da kwayoyin cutar kwamfuta irin su Stuxnet da Flame zuwa ga kwamfutocin cibiyoyin nukiliyan Iran, marubucin ya bayyana cewar: cibiyar leken asirin soji ta HKI da kuma kungiyar leken asirin cikin gida ta Amurka NSI sune suka kirkiro wadannan virus din da nufin lalata kwamfutocin da kuma tattaro bayanan sirri da suke cikinsu.
Ko shakka babu dai Amurka da HKI wani danjuma da danjummai ne a bangaren kulla makirci wa Jamhuriyar Musulunci ta Iran wanda manufarsu guda ce kamar yadda shugabannin Amurkan suka sha fadi a fili da kuma tabbatar da hakan a aikace. Ko shakka babu irin matsayi da tasirin da Iran take da shi a yankin gabas ta tsakiya, haka nan kuma da yunkurin farkawa ta Musulunci da ke ci gaba da kadawa a duniyar musulmi bugu da kari kan ci gaba da shan kashin da Amurka take fuskanta a gabas ta tsakiyar da kuma raunin da HKI ta yi, dukkanin wadannan abubuwa ne da suka sanya Amurka da HKI kara karfafa irin wannan bakar alaka da ke tsakaninsu don cimma bakaken manufofinsu a kan Iran.
Duk da cewa shugaban Amurkan yana nuna irin kokarin da yake yi wajen ganin HKI ba ta yi gaba gadi wajen kawo wa Iran harin soji ba, to amma kuma duk da hakan yana ci gaba da cewa ba su kawar da wannan batu na kawo hari din ba hakan da nufin kara matsin lamba a kan Iran. To amma a fili yake sannan kuma su kansu Amurkawan sun san cewa Iran ba ta nufin mallakan makaman nukiliya. Babbar manufar dukkanin wadannan abubuwa dai ita ce dakatar da Iran daga irin ci gaba mai ban mamaki da take samu a fagen ilimi da fasaha don haka Amurka da kawayen nata musamman HKI suka dauki wannan siyasa ta kashe masanan nukiliya da kuma barazanar kawo harin soji ko za su cimma wannan manufar.
1053300