Bangaren siyasa da zamantakewa, an fitar da mujalla da ake bugawa kan harkoki na yankin gabas ta tsakiya a cikin harshen larabci wadda ta fito a karo na 141 kamar dai yaddad bangaren da ke daukar nauyin buta ya sanar domin amfanin muslumi da kuma sanar das u abin da ke gudana ayankin.
Kamfanin dilalncin labaran iqna ya habarta cewa ya nakalto dagashafin sadarwa na yanar gizo an fitar da mujalla da ake bugawa kan harkoki na yankin gabas ta tsakiya a cikin harshen larabci wadda ta fito a karo na 141 kamar dai yaddad bangaren da ke daukar nauyin buta ya sanar domin amfanin muslumi da kuma sanar das u abin da ke gudana a yankin na gabas ta tsakiya.
Wani harin ta'addanci da aka kai kasar Siriya ta hanyar tarwatsa wata mota da aka makare da bama bamai ya lashe rayukan mutane akalla 12 tare da jikkata wasu da dama.
Majiyar labaran kasar Siriya ta bayyana cewa: Wata mota da aka cika da bama bamai ta tarwatse a yankin Al-Karamatu da ke garin Homs na kasar Siriya, inda harin ya yi sanadiyyar mutuwan mutane akalla goma sha biyu tare da raunata wasu fiye da goma sha biyar na daban.
Tun a watan Maris na shekarar da ta gabata ce gwamnatin Amurka da 'yan korenta na kasashen Larabawa musamman atar, Saudiyya da kuma Turkiyya suke taimakawa 'yan tawayen Siriya, inda daga baya suka fara daukan nauyin tura 'yan ta'adda cikin kasar tare wadata su da makamai domin kifar da gwamnatin Bashar Asad, kuma 'yan ta'addan suna aiwatar da kisan kiyashi kan fararen hula da jami'an tsaro amma kafafen watsa labaran Larabawa da na kasashen Turai suna daura alhakin kisan kan gwamnatin Siriya da nufin tunzura duniya kan daukan matakin soji kan kasar ta Siriya.
1053174