IQNA

Wata Tawagar Bayar Da Agaji Ta Kasar Yeman Ta Isa Ynakin Zirin Gaza

13:38 - July 16, 2012
Lambar Labari: 2369904
Bangaren kasa da kasa, wata tawagar bayar da agaji ta mutanen kasar Yeman ta isa yankin zirin Gaza da nufin kai agaji ga ala'ummar yankin da suke fama da matsaloli sakamakon killacewar da haramtacciyar kasar Isra'ila take yi wa yankin tsawon shekarusama da biyar.
Kamfanin dilalncin labaran iqna ya habarta cewa ya nakalto daga shafin sadarwa na yanar izo na saba cewa wata tawagar bayar da agaji ta mutanen kasar Yeman ta isa yankin zirin Gaza da nufin kai agaji ga ala'ummar yankin da suke fama da matsaloli sakamakon killacewar da haramtacciyar kasar Isra'ila take yi wa yankin tsawon shekaru sama da biyar a kan masaniyar majlaisar dinkin duniya da kungiyoyin kare hakkin bil adama.
Ko shakka babu dai Amurka da HKI wani danjuma da danjummai ne a bangaren kulla makirci wa Jamhuriyar Musulunci ta Iran wanda manufarsu guda ce kamar yadda shugabannin Amurkan suka sha fadi a fili da kuma tabbatar da hakan a aikace. Ko shakka babu irin matsayi da tasirin da Iran take da shi a yankin gabas ta tsakiya, haka nan kuma da yunkurin farkawa ta Musulunci da ke ci gaba da kadawa a duniyar musulmi bugu da kari kan ci gaba da shan kashin da Amurka take fuskanta a gabas ta tsakiyar da kuma raunin da HKI ta yi, dukkanin wadannan abubuwa ne da suka sanya Amurka da HKI kara karfafa irin wannan bakar alaka da ke tsakaninsu don cimma bakaken manufofinsu a kan Iran.
Duk da cewa shugaban Amurkan yana nuna irin kokarin da yake yi wajen ganin HKI ba ta yi gaba gadi wajen kawo wa Iran harin soji ba, to amma kuma duk da hakan yana ci gaba da cewa ba su kawar da wannan batu na kawo hari din ba hakan da nufin kara matsin lamba a kan Iran. To amma a fili yake sannan kuma su kansu Amurkawan sun san cewa Iran ba ta nufin mallakan makaman nukiliya. Babbar manufar dukkanin wadannan abubuwa dai ita ce dakatar da Iran daga irin ci gaba mai ban mamaki da take samu a fagen ilimi da fasaha don haka Amurka da kawayen nata musamman HKI suka dauki wannan siyasa ta kashe masanan nukiliya da kuma barazanar kawo harin soji ko za su cimma wannan manufar.
1053187


captcha