IQNA

Haramtacciyar Kasar isra’ila Tana Fuskantar Matsalolin Siyasa Na Cikin Gida

13:50 - July 18, 2012
Lambar Labari: 2371889
Bangaren kasa da kasa, haramtacciyar kasar Isra’ila tana fuskantar manyan matsaoli na siyasa a cikin gidan da za su iya kaiwa ga rushewarta sakamakon ballewar jam’iyyar yahuadawa mai tsatsauran ra’ayi da ke kokarin ganin ta taka wa pira minister burki kana bin da ta kira sassaucin da yake yi.
Kamfanin dilalncin labaran iqna ya habarta cewa ya nakalto daga shafin sadarwa na yanar gizo, cewa haramtacciyar kasar Isra’ila tana fuskantar manyan matsaoli na siyasa a cikin gidan da za su iya kaiwa ga rushewarta sakamakon ballewar jam’iyyar yahuadawa mai tsatsauran ra’ayi da ke kokarin ganin ta taka wa pira minister burki kana bin da ta kira sassaucin da yake yi wajen hana su daukar makamai da suke kashe palastinawa.
A nasa bangaren shugaban kasar Iran Dakta Mahmoud Ahmadinejad ya ce har abada mafarkin da kasashe makiya jamhuriyar musulunci ta Iran ke yi na ganin cewa sun durkusar da kasar ta hanyar takunkumai da wasu hanyoyi na takurawa ba zai taba kai ga samun nasara ba, Ahmadinejad ya bayyana hakan ne a yau lokacin da yake kaddamar da wata masana'antar kera jiragen kasa a garin Karaj da ke wajen birnin Tehran, yana mai cewa a tsawon shekaru 33 da samun nasarar kafa tsarin musulunci a kasar, ba wata illar da makircin wadannan kasashe ya haifar wa Iran face ci gaba da kuma cusa wa al'ummar kasar ra'ayin dogoro da kai wajen kirkire da kuma kafa masana'antu.
Shugaban na Iran ya ce ko shakka babu kwararri da kuma sauran injiniyoyi na kasar sun taka gagarumar rawa wajen gina kasar da kuma tattalin arzikinta, inda a sakamakon hakan takunkumai da kuma hanyoyi na takurawa da kasashen Turai da Amurka ke amfani da su ba su yi wani tasiri a kan kasar da kuma ci gabanta ba.
1055809

captcha