IQNA

An Yi Kira Ga Kasashen Musulmi Da Su Dauki Matakan dakatar Da Kisan Kiyashi A Myanmar

13:56 - July 19, 2012
Lambar Labari: 2372534
Bangaren kasa da kasa, an yi kira ga kasashen musulmi da su dauki dukaknin matakan da suka dace domin dakatar da kisan kiyashin da ake yi wa mabiya tafarkin addinin muslunci a kasar Myanmar bisa zalunci da nuna wariya da bangaranci gare su saboda su kawai laifinsu mabiya addinin muslunci ne.
Kmafanin dilalncin labaran iqna ya hbarta cewa ya nakalto daga shafin sadarwa na yanar gizo na cewa, kungiyoyin kare hakkin bil adama a kasashen musulmi an yi kira ga kasashen musulmi da su dauki dukaknin matakan da suka dace domin dakatar da kisan kiyashin da ake yi wa mabiya tafarkin addinin muslunci a kasar Myanmar bisa zalunci da nuna wariya da bangaranci gare su saboda su kawai laifinsu mabiya addinin muslunci ne kuma kasashe da ke raya cewa suna manyan musulmi sun yi shiri da bakunansu.
Jamhuriyar Musulunci ta Iran ta yi Allah wadai da kashe ministan tsaron kasar Siriya tare da mika ta'aziyyarta ga gwamnati Siriya da al'ummar kasar.
Shugaban bangaren kula da kasashen Larabawa da Afirika a ma'aikatar harkokin wajen kasar Iran Husain Amir Abdul-Ilahiyon ya yi tofin Allah tsine kan harin ta'addancin da aka kai birnin Damasqas fadar mulkin kasar Siriya a jiya laraba, harin da ya yi sanadiyar mutuwar manyan jami'an tsaron kasar ciki har da ministan tsaron Siriya.
Amir Abdul-Ilahiyon ya kuma bayyana cewa; wadanda suke aikewa da makamai tare da goyon bayan ayyukan ta'addanci a kasar ta Siriya da yardan Allah ba zasu taba cimma nasara ba.
A gefe guda kuma ministan harkokin wajen kasar Iran Ali Akbar Salihi ya yi ta'aziyyar kashe ministan tsaron Siriya da sauran manyan jami'an kasar ga takwaransa na Siriya Walid Mu'allim.
Har ila yau mataimakin shugaban kasar Iran Muhammad Ridha Rahimi ya mika sakon ta'aziyya ga fira ministan kasar Siriya, tare da jaddada cewa wannan hare haren ta'addancin da ake kai wa kan kasar ba zai taba raunana gwamnatin Siriya kan yakin da take yi da ayyukan ta'addanci ba.
1056819
captcha