Kmafanin dilalncin labaran iqna ya ahabrta cewa ya nakalto daga shafin sadarwa a yanar gizo cewa, masana da malamai da dama sun amanar cewa babban aikin da ke gaban cibiyar ahlul bait ta duniya shi ne shiga kafar wando daya da akidar kafirta usulmi ta wahabiyanci da ke ci gaba da yaduwa a duniyar musulmi wanda hakan shi ne bababn hadari da ke fusknatar musulmi tare da gurbata a kidarsu da kuma bata sunansu a idon duniya sakamakon ayyukan ta’addancin da amasu dauke da wannan akida suke aikatawa a duniya.
Tare da wanna matsayin da kasashen Rasha da kuma china suka dauka, kokarin da kasashen yamma tare da wasu kawayensu a kasashen larabawa na kara takurawa gwamnatin kasar Syria ya kasa kai labara, sa'o'ee kadan, kafin a fara kada kuri'a kan wannan bukatar a komitin, shugaban kasar Amurka Barak Obama ya kira tokwaransa na kasar Rasha Vlidemir Putin ta wayar tarho inda ya yi kokarin gamsar da shugaban na kasar Rasha kan bukatar amincewa da wannan kudirin.
Kasashen Rasha da China dai sun bayyana cewa kudurin da kasashen yamma suka gabatar yana nuna goyan baya ga bangare guda ne cikin bangarorin da suke riciki a kasar ta Syria, wato yan tawayen kasar, wadanda kuma suka dauke da makamai kuma suke samun tallafi daga wadannan kasashe.
Jakadan kasar Rasha a komitin, ya kara da cewa, kudirin ya yi hannun riga da yarjejeniyar Geneva ta warware rikicin kasar Syria ta hanyar tattaunawa, har'ila yau bukatar ta yi watsi da shawarar Kofi Annan, tsohon babban sakatarin MDD, kan warware rikicin na kasar Syria, mai bukatu 6.
Kasashen Amurka, Britani, Faransa da kuma Jamus ne suka gabatar da wannan bukatar, a karkashin sashe na 7 ko kuma ( Chapter 7) na kundin tsarin aikin MDD, wanda ya bawa memebobin komitin tsaron majalisar 15 damar amfani da hanyoyin diblomasiya, takunkumin tattalin arzi ko kuma karfin soje don wanzar da zaman lafiya a duniya. Bukatar kasashen dai, ya tanaji cewa gwamnatin shugaba Bashar Al-asad ta dakatar da bude wuta kan fararen hula, ta janye jami'an tsaronta daga dukkan garuruwa da anguwannin a duk fadin kasar cikin kwanaki 10, idan ta kaza yi haka, to suna da zabin fada mata da karfin soja.
Kasashen Rasah da china dai sun ce, amincewa da wannan bukatar, kamar sake bawa kasashen yamma damar kai farmaki soje ne kan kasar Syria, kamar yadda suka yi a kasar Libya a shekarar da ta gabata.
Komitin tsaro na MDD, a shekarar da ta gabata, ya amincewa kasashen yamma shata yankin hana shawagi da jiragen sama a kasar Libya da nufin kare fararen hula wadanda sojojin Kazzafi suke kaiwa hare hare da jiragen saman, amma sai suka yi amfani da wancan damar, suka fara kai hare hare kan cibiyoyin tsaron gwamnatin kasar Libya. Suka kuma rika tallafawa yan tawayen kasar wadanda suka kifar gwamnatin Kazzafi a cikin yan watanni. Sannan bayan faduwar gwamnatin Kazzafi, suka yi watsi da bukatun kasashen na Rasha da China a kasar Libya.
1057792